Yace muna a nan birnin Fall River a jihar Massachusetts, birni da Amurka ke alfahari da ita wanda bakin haure suka ginata.
Yace munga tattalin arziki da saka jari yayi tashin goron zabi, amfani masu zuba jari yayi kauri, kampanoni suka samu kazamin riba amma kuma suka gaza raba amfani ga ma’aikata.
Mun ga gwamnati da tayi ta fifitukar ganin ta ci gaba da gudanar da aiyukanta.
Kasar Rasha kuma ta zo tayi dumu dumu ta shiga ko kuma ta yi katsalanda a demokaradiyarmu
Yace ana yaki a kan kare muhalli.
Ya ci gaba da cewa, za a iya yin shewa ga alkauran da yan siyasa suka dauka, amma kuma za a yanke wa kasa hukunci ne a kan alkauran da ta cikawa jama’arta.
Facebook Forum