Wata girgizar kasa mai karfi maki 6.4 ta ratsa tsibirin Lambok na kasar Indonesia kuma ta kashe akalla mutane goma kana wasu arba'in suka jikata.
An bude zabe a Cambodia inda 'yan kasar zasu zabi wakilan majalisar kasa 125, a cikin wani tsarin zaben da ya sha sukar lamiri, sakamakon rashin masu adawa ga jami’iyar Cambodina People’s Party mai mulkin kasar.
Kungiyar Taliban ta tabbatar da tattaunawa da Amurka kai tsaye a Qatar a cikin wannan mako da zummar kawo karshen yakin shekaru 17 a Afghanistan.
Wasu kungiyoyi sun maida hankali a kan matasa a Zimbabwe su shiga zaben kasar na farko, bayan saukar Robert Mugabe daga mulki da za a yi a ranar Litinin, wanda batun rashin ayyukan yi da tabarbarewar siyasa zasu zama batutuwar da masu kada kuria zasu mai da hanakali a kai.
Batun haraji shine kan gaba a tattaunawa da shugaban Amurka Donald Trump zai yi da shugaban zartarwar kungiyar Taryyar Turai Jean-Claude Juncker a yau Laraba.
Kafofin yada labarai a Amurka sun buga wani faifai a jiya Talata, wanda a ciki aka ji shugaba Donald Trump da dadadden lauyansa Micheal Cohen suna tattauanawa a kan yiwuwar biyan wata mai tallar sutura a kan batun Trump ya taba amfani da ita.
An kashe akalla mutane 31 kana wasu 40 sun jikata a wata fashewa, a runfar zabe a kudu maso yammacin Pakistan a yau Laraba, bayan wasu sa’o’i da fara kada kuri’ar zaben wakilan majalisar dokoki.
'Yan adawar kasar Kamaru sun gaza gabatar da dan takara daya tilo da zai iya fafatawa da shugaban kasar Paul Biya wanda ya kwashe shekaru 36 yana mulkin kasar. Yan takara 28 zasu fafata a zaben shugaban kasa na ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ake sa ran Biya zai lashe.
Shugaban Demokaradiyar Jamhuriyar Congo Joseph Kabila yace za a gudar na zaben shugaban kasa a ranar 23 ga watan Disamba, amma kuma bai yi wani karin bayani game da shirinsa ga zaben ba.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya ce Amurka ba za ta tura wani dan Amurka zuwa kasar Rasha domin a yi masa tambayoyi a kan tuhumar hada hadar fidda kudade ta barauniyar hanya.
Wani farmaki ta sama ya kashe akalla mutane 54 ciki har da mayakan IS da kuma fararen hula 28 a gundumar gabashin Syria ta Deir Ezzor a cewar masu sa ido a kan take hakin bil adama.
Dadadden shugaban kasar Kamaru Paul Biya, ya sanar da zai sake shiga takarar shugabancin kasar na wani sabon wa’adi.
Jami'ai a India sun ce wani gungun maza sun kama wasu mata guda biyar masu aikin taimako suka musu fyade da bindiga a wani kauye dake gabashin gundumar Jharkhand.
Hukumomi a Amurka sun hada wata ‘yar kasar Guatemala da dan ta mai shekaru bakwai a yau Juma’a bayan an raba su watanni da dama a kan iyakar Amurka.
Shugaban Eritrea yace zai tura tawaga zuwa Habasha domin tattaunawa a kan alkawarin da shugaba Firai Ministan Abiy Ahmed ya dauka na aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a shekarar 2000
Wani hari da Taliban ta kai da sanyi safiyar yau Laraba a gabashin Afghanistan, ya kashe mutane 30 a cikin rundunar gwamnati, mummunar hari tun bayan da aka tsagaita bude wuta na wucin gadi domin gudanar da bukuwar karamar Sallah.
Masu zanga zanga a Amurka sun bayyana fushi da damuwarsu ga gwamnatin Trump, a kan shirinta na raba ‘ya'yan bakin haure da iyayensu.
Kungiyar kwallon kafa ta kasa da kasa ta bada izinin daukar bakwancin gasar cin kofin duniya a shekarar 2026 ga Canada da Mexico da kuma Amurka su yi hadin gwiwa wurin shirya gasar.
Kasar Italiya ta gayyaci jakadar Faransa a yau Laraba a wani matakin mayar da martani ga kalaman shugaban Faransa Emmanuel Macron inda ya kushewa gwamnatin Italiya sibili da korar daruruwar bakin haure da aka ceto a cikin jirgin ruwa.
Domin Kari