A cikin shari’ar da Amurka ke yiwa wasu mutane biyar dake gidan yarin Amurka dake Guantanamo, wanda ake zarginsu da hannu a cikin harin ta’addanci a ranar 11 ga watan Satunban 2001, wani alkalin sojoji ya umarci lauyoyin gwamnati kada su yi amfani da bayanan suka yiwa hukumar FBI, a cikin tambayoyi.