Ya dauki rantsuwar kama aiki ne a yau Lahadi a gaban dubban 'yan kallo a filin wasa a babban birnin kasar Harare.
Lokaci ya yi da yakamata mu hada kai mu tafi tare, inji Mnangagwa mai shekaru 75 a wurin bukin rantsar da shi.
Zaben da Mnangagwa ya lashe a wata da ya gabata, shine na farko a cikin shekaru da dama da aka yi ba tare da dadden shuagaban kasar Robert Mugabe a ciki ba, kuma madugun 'yan adawan kasar Nelson Chamisa shine dan takarar babban jami’iyar adawa ta Movement for Democratic Change a zaben.
Mnangagwa ya samu kashi 50.8 cikin dari na kuru’un, amma kotu ta dakatar da rantsar da shi saboda wata kara dake gabanta. Shiko shugaban 'yan adawa Chamisa da ya samu kasha 44 cikin dari, yace shine ya lashe zaben.
A shekaranjiya Juama’a ne kotu ta amince da nasarar da Mnangagwa ya yi da karamin rata.
Facebook Forum