A wani mataki na ba saban ba, shugaban hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Michelle Bachelet ta bukaci gwamnatin Burundi ta roki gafara a kan kalaman batanci da ta yiwa mambobin hukumar bincike mai zaman kanta, lamarin da ya zubar da mutuncinsu.
Ana sa ran mutumin nan da aka kama kuma aka caje shi a ranar Juma’a da aika da akalla kunshi 13 dauke da abubuwar fashewa zuwa ga masu sukar lamirin shugaban Amurka Donald Trump, zai fara bayyana a gaban kotu, a cewar wasu rahotanni daga jami’an tsaro.
Wani mutumin da yake ihu yana cewa, duk wadannan Yahudawa yakamata su mutu, ya shiga wani wurin bautar Yahudu a Pittsburg a jiya Asabar, ya fara harbin kan mai uwa da wabi ya kashe mutane 11, kuma wannan ne kisar bindiga na baya a nan Amurka.
Jami’iyun adawan Demokaradiyar Jamhuriyar Congo da kansu ke rarrabe, sun sanar a jiya Juma’a cewa zasu shiga zaben watan Disemba da suke kalubalanta kuma sun ce zasu fitar da dan takara daya kafin ranar 15 ga watan Nuwamba, ana saura makwanni shida da yin wannan muhimmin zabe.
Hukumomi a Amurka sun ce an kama wani mutumin da aka dade ana samunsa da aikata laifuka a jihar Florida a jiya Juma’a, kuma an same shi da aika akalla kunshi 13 masu dauke da abubuwar fashewa zuwa ga masu sukar lamirin shugaba Donald Trump.
Gwamnatin jahar Kaduna tace mutane biyar ne aka kashe sakamakon rikicin da ya tashi a wasu sassan jihar ranar Lahadi, kuma an kama mutum uku da ake zargi da hannu kan rikicin.
An kashe mutane 15 kana wasu 60 sun jikata a jiya Asabar, yayin da wani dan kunar bakin wake ya yi yunkurin shiga wata runfar zabe a arewacin Kabul.
Kasashen Faransa da Jamus sun yi Allah wadai da kashe dan jaridar Saudiya Kamal Kashoogi a cikin ofishin jakadancin Saudi Arabia a Istanbul.
Jami’ai a Najeriya sun tabbatar a jiya Asabar cewa an kashe mutane hamsin da biyar a cikin wata arangama tsakanin matasan Krista da Musulmi a Arewacin Najeriya.
Wani sabon rahoton Majalisar Dinkin Duniya (MDD), yana kira ga sake daruruwar mutane da aka sace su a Sudan ta Kudu a lokacin rikicin tsakanin ‘yan tawaye da gwamnatin kasar.
Wani ayarin bakin haure daga nahiyar tsakiyar Amurka sun karya katangar kan iyakar Guantemala a jiya Juma’a suna kokarin tasarwa shingen ‘yan sandan a Mexico, wanda gwamnatinta ta yiwa Amurka alkawarin tare ayarin bakin hauren.
Saudi Arabia tace sakamakon binciken farko da ta gudanar a kan bacewar dan jaridar Saudiyar nan Kamal Kashoogi, ya nuna ya mutu a ofishin jakadancinta a Istanbul bayan fada da ya yi da mutane da ya same su a wurin, a cewar ma’aikatar labaran kasar.
Tsohon mataimakin Firai Ministan Malaysia Anwar Ibrahim ya karfafa dawowarsa a cikin harkokin siyasar kasar, inda ya yi nasara a zaben majalisar dokokin kasar a jiya Asabar.
Wasu fashewa guda biyu a gari Baidoa na Somalia sun kashe akalla mutane 15 kana wasu 30 kuma sun jikata.
Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a jiya Asabar cewa baya jin dadin abin dake faruwa game da bacewar dan jaridar Saudi Arabia Jamal Kashoogi, yana mai cewar tana yiwuwa an kashe shi.
Faston nan ba-Amurke da kasar Turkiya ta sake shi bayan ya yi zaman gidan yari tsawon shekaru biyu, ya gurfana a gaban shugaban Amurka Donald Trump a ofishinsa na Oval Office a fadar White House a jiya Asabar kuma ya yiwa shugaba Trump addu’a Allah kara masa hikima.
Wani ma’aikacin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) a gabashin Demokaradiyar Jamhuriyar Congo, ya kamu da cutar ebola a karon farko, tun lokacin da cutar ta barke, a cewar shugaban dakarun kwantar da tarzoma ta MDD.
Sakataren bitalmalin Amurka Steve Mnuchin, ya fada a jiya Juma’a cewa yana kan bakarsa na halartan babban taron zuba jari a kasar Saudi Arabi a karshen wannan wata, duk da tarin shaidar dake nuna an kashe dan jaridar Saudiyar a ofishin jakadancin Saudi Arabia a Istanbul a Turkiya.
Wata kotun Turkiya ta saki wani ba-Amurke fasto, Andrew Brunson, lamarin da ya kawo karshen tankiyar diflomasiya tsakanin Washington da Ankara.
Domin Kari