Rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan kungiyar Boko Haram sun yi shigan burtu inda suka so kai farmaki kan wata makaranta dake Kafin Hausa wajen Bakin Dutse dake yankin na Madagali, to sai dai ‘yan Sakai na maharba sun samu nasarar tarwatsa su.
Komitin da gwamnatin jahar Pilato ta kafa domin maida ‘yan gudun hijirar jihar zuwa garuruwansu na asali ya gano cewa fiye da mutane dubu hamsin da tara ne rikicin da ya auku a kananan hukumomi biyar na jihar ya shafa yayinda mutane dubu hamsin da dari biyu da goma sha biyu ke gudun hijira.
Hukumomi a Somalia suna binciken mutuwar wasu fararen hula hudu da aka ce rundunar kwantar da tarzoma ta kungiyar Tarayyar Afrika sun kashe a jiya Talata, bayan fashewar wani bam a gefen hanya dake auna ayarin rundunar zaman lafiyar.
Kungiyoyin yaki da bauta a jamhuriyar Nijer sun yi na’am da matakin dakatar da kasar Mauritania daga sahun kasashen dake amfana da tsarin sassaucin haraji na AGOA wanne ke ba kasashen Afirka damar shigarda da kaya zuwa Amurka ba tare da biyan haraji ko kudaden awo ba.
Gwamnatin najeriya da kungiyoyin kwadagon kasar sun cimma yarjejeniyar amincewa da mafi karancin albashi na Naira dubu talatin, lamarin da ya kai ga tada jijiyoyin wuya tsakanin bangaren ma’aikatan da hukumomin Najeriya.
Babbar Kotun Kano ta umarci majalisar dokoki ta jihar ta dakata da binciken zargin rashawar Dala miliyan biyar akan gwamna Abdullahi Umar Ganduje, har sai ta saurari karar da wasu lauyoyi suka shigar gaban ta. sai dai majalisar tace ba ta kai ga samun wannan umarni ba.
Wani lauya dan kasar Pakistan da ya taimakawa wata mace ‘yar Krista da kotu ta janye hukuncin kisar dake kanta biyo bayan kalaman sabo da tayi game da Manzon Allah.
‘Yan sanda a jiya Asabar sun gano mutumin nan da ya kashe wasu mata biyu a wani wurin motsa jiki wato Yoga studio dake Tallahassee na jihar Florida kafin ya kashe kansa.
‘Yan Kasar Morocco suna kara karuwa da sauran ‘yan Afrika suna shiga bulaguron nan mai cike da hatsari zuwa kasar Spain, saboda abin da suka kira tabarbarewar rayuwa da kuma kuntatawan ‘yan siyasa.
Wata tawagar gwamnatin Pakistan ta cimma matsaya da wasu kungiyoyin Musulmi a kan dakatar da wata gagarumar zanga zangar kwanki uku na nuna kalubalantar hukuncin kotun koli da ta saki wata ‘yar Krista da tayi kalaman sabo ga Manzon Allah.
Sauran kwanaki kalilan a yi zaben rabin wa’adi a Amurka kuma a wannan lokaci ana kara samun fargabar cewa Rasha zata iya sake yin katsalandan a harkar demokaradiyar Amurka daga yanzu har izuwa zaben shugaban kasa a shekarar 2020.
Shugaban Amurka Donald Trump yana kara gangami a kan yunkurinsa na soke dokar da take baiwa yaran da aka haifa a Amurka ‘yancin zama dan kasa, yayin da dubban bakin haure suke karasowa a hankali zuwa iyakar kudancin Amurka.
Ma’ikatan kamfanin Google a fadin duniya sun yi yajin aiki domin kalubalantar yanda kamfanin ke daukar batun neman yin lalata da mata.
Shugaban Amurka Donald Trump da uwargidansa Melania Trump sun kai ziyara a wurin ibadar Yahudawa a Pittsburgh, inda wani dan bindiga ya kashe mutane 11 a ranar Asabar da ta shige yayin da suke ibada
Jami’an tsaron kasar Kamaru na kaiwa masu fita tituna suna zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da zaben 7 ga watan Oktoba hari. Domin kare kansu daga duka ko kamu, masu zanga-zangar sun dauki sakonsu zuwa makarantu ko wuraren ibada.
Cesar Sayoc, Mutumin da ake ake zargi da aika sakonni 13 masu dauke da bama bamai zuwa ga masu sukar lamirin shugaba Donald Trump, yana da jerin sunayen mutane sama da 100 da yake shirin aunawa, a cewar jami’an Amurka.
Yau Talata shugaban Amurka Donald Trump da uwargidansa Melania zasu ziyarci birnin Pittsburg, kwanaki uku bayan da wani ‘dan bindiga ya bude wuta a wani wajen ibada a birnin.
Hukumomi a jamhuriyar Nijer, sun bayyanar da kididiga a kan ibtila’in da ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka samu bana a sassa daban - daban na kasar.
Kungiyar lauyoyi mata ta kasa da kasa reshen jihar Kano ta nuna damuwa kan yadda aka yi amfani da daliban makaratun Pramare wajen gudanar da zanga zanga lokacin da majalisar dokokin jihar Kano ta fara binciken batun zargin gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje da karbar cin hanci daga 'yan kwangila.
Taron kungiyar kiristoci ta Najeriya ta CAN reshen jihohin arewa 19 a Abuja ya wayar da kan mabiya muhimmancin hakuri da gudanar da bincike na adalci kafin daukar wani mataki a yayin da duk a ka samu wani akasi.
Domin Kari