Hukumomi a Ghana sun bayyana fargabar samun hare haren ‘yan ta’adda a cikin wannan lokaci, lamarin da yasa hukumomin tsaron kasar suka fara daukar matakan sa ido a kan harkokin jama’a tare da yin gargadi ga jama’a su kula kuma su taimakawa jami’ai da bayanai.
A yau Talata goma sha daya ga watan Yunin shekarar dubu biyu da ashirin ne majalisar dokokin Najeriya ta ciko tara zata fara aiki, baya an zabi shuganannin majalisar.
Shugabannin masu zanga zanga a Sudan suna kira ga mutanen kasar su kara kaimi a ayyukan kalubalantar gwamnatin sojan kasar, biyo bayan amfani da karfin tuwo da sojojin suka yi a kan mutane a lokacin wani zaman dirshe.
Firai Ministan Pakistan Imran Khan ya aikawa takwarar aikinsa na India Narendra Modi da wasikar dake kira ga shirya zaman sasantawa tsakanin su.
A ‘yan kwananki masu zuwa ne majalisar tarayyar Amurka zata fara sauraren bahasi a kan rahoton bincike da Robert Muller ya gudanar a kan ko kasar Rasha tayi katsalandan a zaben shugaban kasar Amurka a shekarar 2016.
A jiya Juma’a an zabi wasu kasashe biyar da zasu yi aiki a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya(MDD) tsawon shekaru biyu. Kasashen sun hada da Estonia da Jamhuriyar Nijer da Saint Vincent and Grenadines da Tunisia da kuma Vietnam.
Shugaban Amurka Donald Trump yace Amurka da Mexico sun cimma yarjejeniya a kan batun bakin haure domin dakatar da haraji a kan kayan Mexico.
Amurka tayi kira ga gwamnatin kasar China a kan yadda take tauye hakkin wadanda suka yi zanga zangar lumana a dandalin Tiananmen a ranar hudu ga watan Yuni shekarar ali dari tara da tamanin da tara(1989) inda aka yi masu kisan kiyashi.
Mazauna yankunan Yamai da Dosso da Tilabery sun fada cikin mawuyacin halin rayuwa a sakamakon daukewar wutar lantarki da ake huskanta yau kimanin kwanaki uku, matsalar da kamfanin wutar lantarki Nigelec ya danganta da faduwar wasu karafunan tangarafu tsakanin birnin Kebbi da birnin Gaure.
Al’ummar jihar Filato sun bayyana fatar gwamnan jahar Simon Lalong zai aiwatar da tsare tsare da zasu kawo ci gaban jahar. Al’ummar jihar sun bayyana hakan ne a hira da suka yi da sashen Hausa na Muryar Amurka.
Mai bincike na musamman kan batun yin katsalandan da Rasha ta yi a zaben shugaban kasar Amurka na shekara ta dubu biyu da goma sha shida Robert Muller karon farko ya yi jawabi ga al'ummar Amurka ,ya kuma bayyana cewa, ba zai fadi wani abu da ya shige bayanin da ya yi ba dangane da batun
Yayin da dalibai a kasar Kamaru suka fara rubuta jarabawar shekara shekara, jiya Litinin, daruruwan malaman su a yankin da ake amfani da harshen turancin Igilishi sun shiga tituna suna zanga zanga.
Zaben shekarar 2019 yazo da abubuwan ban al’ajabi da kuma mamaki da suka hada har da kwace mulki daga hannayen jam’iyu dake mulki suka koma hannun jam’iyun adawa kamar yadda suka faru a jihohin Bauchi dakuma Gombe da wasu wurare a Najeriya.
A yau ne ministocin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ke ajiye aiki biyo bayan kawo karshen wa’adin gwamnatin a zangon farko. Masana da dama sun yi fashin baki a kan rawa da ministocin gwamnatin Najeriya suka taka, a wannan gwamnatin mai barin gado.
Biyo bayan kisan gilla da kona garuruwa da ‘yan bindiga suka shafe mako guda cur suna yi a Barsari, a yammacin jiya shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari a kan batu da ya jefa talakawan jihar cikin rashin kwanciyar hankali.
Kasashen Afrika ta Gabas suna shirin haramta shiga da sabulan wanka ko man shafawa ko kuma wani abu mai dauke da sanadarin hydroquinone, wanda ke sa mutum ya zama baturen karfi da yaji, sanadari dake tattare da matsalolin lafiya masu yawan gaske.
A wata zaman da aka saba yi a dakin Roosevelt a fadar White house a jiya Alahamis, a kan sanar da tallafin kudi dalar Amurka biliyan sha shidda ($16b) ga manoma, ya rikide ya koma zaman cin mutuncin tawagar manyan ‘yan Democrats a majalisar tarayya da shugaban kasa ya musu.
Sakataren tsaro mai rikon kwarya Patrick Shanahan, ya karyata rahotanni dake cewa za a aika dakarun Amurka dubu biyar zuwa dubu goma zuwa yanki Gabas ta Tsakiya domin dakile barazanar da Iran ke yi.
Kungiyar Kiristoci ta Nigeriya CAN ta tabbatar da labarin kama daya daga cikin malaman addinin Krista da mabiya goma sha biyar a yankin Birnin Gwari dake Kaduna.
Wani kakakin gwamnatin Jamhuriyar Nijar yace an kashe a kalla sojoji goma sha bakwai yayin da wadansu goma sha daya kuma suka bace bayan da wadansu mahara da ba a san ko su wanene ba suka yi masu kwantan bauna.
Domin Kari