Hukumar kula da lamuran ruwan sama da na koguna NIHSA ta anakaradda jihohin Najeriya 15 cewa za a samu ambaliyar ruwa a cikin su da hakan tuni ma har ya haddasa asarar rayuka.
Yayin da dokar hana kai-komo, irin wadda yankin Kashmir bai taba gani, ke ci gaba da aiki, Firaministan Indiya Narendra Modi ya yi wa ‘yan yankin na Kashmir alkawarin fara shiga, abin da ya kira, “sabuwar makoma.
Jiya Alhamis, magadan gari sama da 200 a Amurka, sun bukaci ‘yan majalisar dattawa da su dawo daga hutun lokacin barazar "Summer", su rattaba hannu kan kudurin dokar dakile wanzuwar bindigogi.
A ranar Laraba da safe ne aka yi ta tada jijiyar wuya a zauren majalisar dokokin kasar Kenya bayan da wata ‘yar majalisa Zuleika Hassan ta shiga zauren majalisar da jinjirin wata biyar.
Da ya ke mai da martani kan hare-haren kan mai uwa da wabin nan da aka kai a Amurka, Shugaban Amurkar Donald Trump ya sha alwashin, abin da ya kira, daukar matakin gaggawa.
Daruruwan mutane ne a kasar Kamaru suka yi zanga-zanga a babban birnin kasar, suna neman sanin inda aka kai fursinonin da aka sauyawa waje a makon da ya gabata, biyo bayan wani bore da ya barke a babban gidan yarin birnin Yaounde.
A yayin da wasu ke shirin shiga zanga-zangar juyin juya hali a Najeriya, hadakar kungiyoyin matasan Arewacin Nigeriya mai suna Coalition of Northern Groups ta ce kada wani dan Arewa ya shiga zanga-zangar don akwai lauje cikin nadi.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta girke jami’anta a muhimman sassa kamar mahadar tituna don rigakafin gudanar da zanga-zangar juyin juya hali daga wasu kungiyoyin da’awar tsaro da dimokradiyya.
An kashe wasu sojojin Amurka biyu a bakin daga, a wani al'amarin da ake ganin irin harin nan ne na sojoji masu canza sheka.
Shugagan Amurka Donald Trump na cigaba da dulmuya cikin abin da masu sukarsa ke kira take-taken nuna banbancin launin fata, inda ya auna birnin Baltimore mai rinjayen bakaken fata, da kuma wani fitaccen mai wakiltar birnin a majalisar dokokin tarayyar Amurka mai suna Elijah Cummings,
A daidai lokacinda Majalisar Dattawan Najeriya na dab da kammalla tantance Ministoci 43 da Shugaban Kasa ya aika mata, jama'a naci gaba da cece kuce akan yadda yayi nadin Ministocin da kuma yadda suke amsa tambayoyi ba tare da an san ma'aikatun su ba.
A kalla mutane goma 17 suka mutu a wani bam da ya tashi a cikin mota a Mogadishu a jiya Litinin, a wani rahoto da ya tabbatar wa sashen Somali na Muryar Amurka.
Dubban masu zanga-zanga sun yi dafifi a babban titin Puerto Rico, su na ta kiran da Gwamna Ricardo Rossello ya yi murabus daga mukaminsa.
Harkoki sun tsaya cik saboda yajin aikin gargadin da ’yan kungiyar keke-napep suka faro a Adamawa, dominn nuna fushi a kan wata sabuwar doka ta amfani da lasisin tuki wanda hukumar kiyaye hadura a Najeriya, Federal Road Safety Commission (FRSC), ta kaddamar a kan kudi Naira dubu hudu da dari daya.
Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore tace shirin nan da gwamnatin tarayya ta bullo dashi na tsugunar da makiyaya waje guda da tayi wa lakabin Ruga, ya janyo rudani a tsakanin makiyaya a fadin Najeriya saboda rashin sanin alkibilar shirin.
Mutuwar wakilin gidan talbijin na Channels, ya kai adadin mutanen da suka mutu a bangare da ban a ‘yan Shi’a zuwa mutum biyu, sakamakon samun raunuka yayin wata arangamar ‘yan Shi’a almajiran Ibrahim Elzakzaky da ‘yan sanda a birnin tarayya Abuja.
Wuni guda bayan ya bada bahasi game da halin da ake ciki a kan iyakar Amurka gaban ‘yan majalisar dokokin, shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Homeland Security, ya kama hanyarsa zuwa kan iyakar Amurka da Mexico a karo na hudu a cikin ‘yan makwanni.
Majalisar Dinkin Duniya (MDD) tace tsananin karancin abinci da ake fama da shi a Zimbabwe yanzu ya kai ga bukatar agajin gaggawa. Tace yawancin al’umman kasar basu samun abinci saboda yawan sauyin yanayi da ya janyo fari da kuma durkushewar tattalin arziki da kasar ke huskanta.
Adadin ‘yan jarida da aka kashe a kan aikinsu a shekarar 2018, ya ninka abin da aka gani a shekarar 2017 a cewar wata kungiya mai zaman kanta a nan Amurka ta Committee to Protect Journalists.
Kasar Iran ta yi barazanar farfado da shirinta na nukiliya zuwa matakin da ya ke kafin ta rattaba hannu a yarjajjeniyar 2015 da manyan kasashen duniya shida.
Domin Kari