'Yan majalisu dokokin Amurka guda hudu na Jam’iyar Democrats sun bayyana gaban manema labarai, a wani matakin bai daya na nuna jajircewa da yin tir da caccakar su da Shugaba Donald Trump ya yi ta kafar sada zumunta da kuma ta baka.
Dubun wasu masu garkuwa da mutane da fashi da makami, ya cika, bayan hukumar tsaron a’lumma wato Civil Defence a jahar Nasarawa ta kara kaimi wajen zakulo bata gari dake cutar a’lummar jahar.
Masana Shari'a da kwararru kan tsaro na cigaba da tattauna batun cigaba da tsare jagoran mabiya Shi'a a Najeriya Sheik Ibrahim El-zazzaky.
A yau Lahadi ake sa ran jami’an hukumar shige da fice da ayyukan kwastam ta Amurka zasu kaddamar da wani aikin kamen bakin haure dake cikin kasar wanda a baya hukuma ta nemi su bar kasar.
Mazauna birnin New Orleans na jihar Louisiana a nan Amurka, sun kara kaimi wurin sayin kayan aiki domin inganta gidajen su da basu kariya daga mahaukaciyar guguwar nan ta Barry dake bugowa daga tekun Mexico.
Kasar Zimbabwe tana husakantar karancin wutar lantarki mafi muni a ‘yan shekarun nan, lamarin da ya kai ga ma’aikata suka koma aikin dare, lokaci kadai da ake samun wutar lantarki.
Hukumar sa ido kan harkokin Nukiya ta Majalisar Dinkin Duniya, ta tabbatar cewa Iran ta zarce adadin da aka kayyade mata na inganta sinadarin Uranium, a karkashin yarjejeniyar nukiliya aka cimma da ita a shekarar 2015.
Kasar Kamaru ta ce wasu ‘yan kalilan ne kawai daga cikin ‘yan gudun hijirar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dinnan 285,000 su ka amince su koma kasarsu.
Yayin da kananan hukumomi a Najeriya suka fara karbar kason su na kudade aiwatar da ayyuka kai tsaye daga asusun tarayya a watan daya gabata na Yuni, gwamnonin jihohin sun janye tallafin da sukan yiwa kananan hukumomin.
‘Yan kungiyar Shi’a almajiran Ibrahim Elzakzaky sun kaddamar da sabuwar zanga zanga don neman gwamnatin Najeriya ta ba da dama a kai malamin asibiti a kasar waje saboda yana fama da tsananin rashin lafiya.
Askarawan tsaron gabar tekun Tunisia a jiya Asabar sun tsamo gawarwaki 14 na bakin haure ‘yan Afrika da suka niste a cikin jirginsu dake dauke da mutane 80 a lokacin da suka taso makwabciya Libya zuwa Turai, inji hukumar Red Cross ta Tunisia.
Jami’ai sun fara taruwa a babban birnin Jamhuriyar Nijar a karshen wannan mako domin fara taron kolin Tarayyar Afrika wanda zai tattauna a kan dadadden shirin da nahiyar ke niyar aiwatarwa na kulla huldar cinikayya tsakanin kasashen nahiyar.
Rahotanni daga Sudan na nuna cewa akalla mutane 11 aka kashe a yayin zanga zangar baya bayan nan ta neman a koma mulkin farar hula a kasar.
A jiya Litinin wasu maza biyar dauke da makamai su ka kai wani mummunan hari da wata mota mai shake da bama-bamai sannan suka shiga barin wuta da bindigogin su a Kabul, babban birnin kasar Afghanistan, inda suka hallaka akalla mutum guda baya ga wasu da dama da su ka raunata.
An dai shafe kusan makwanni biyu da kafa dokar hana fitan tun daga maraice zuwa karfe shida na safe musamman a Jalingo fadar jihar Taraban.
Hukumomi a jihar Inugun Najeriya sun musanta rade-radin cewa an kori Fulani makiyaya daga garin Nenwe dake karamar hukumar Aninri na jihar, inda kuma hukumomin suka yi ittifakin cewa wannan mumunan sharri ne daga 'yan tada zaune tsaye.
Amurka ta kakaba takunkumai a kan dan shugaban Venezuela Nicholas Maduro, wani sabon mataki da Amurka ta dauka a kokari da take yi domin hambarar da shugaban kasar mai ra’ayin 'yan gurguzu.
Amurka tayi kira ga jami’an tsaro da sojojin kasar Sudan cewa kada su yi amfani da karfin tuwo a kan wadanda zasu gudanar da gagarumar zanga zanga a gobe Lahadi talatin ga wata Yuni.
Domin Kari