An bude Cibiyar zamani ta horas da mata dabarun kiwon lafiya a matakin farko a jami’ar Bayero, a kokarin samar da ma’aikatan lafiya mata musamman a yankunan karkara, da ake sa ran wannan shirin hadin gwiwa zai kawo karshen yawan mace macen mata masu juna biyu a jihar.
‘Yan sandan jihar Connecticut na nan Amurka sun harbe wani matashi dan asalin kasarGhana har lahira a West Haven, Mubarak Suleman ya mutu ne bayanda ‘yan sandan suka harbe shi sau bakwai.
Dubun dubatan ‘yan kasar Malawi ne suka fita zanga-zanga a jiya Alhamis, domin nuna kin amincewarsu da yunkurin da wasu suke yi na baiwa masu shari’a cin hanci a kan wata shari’ar da ake yi don kalubalantar sake zaben shugaba Peter Muthirika a bara.
Kasar Sudan na daga cikin kasashen da suka fi fama da talauci a duniya. Tashin gwauron zabi da farashin kayan masarufi suka yi ya janyo zanga-zangar da ta yi sanadiyyar hambare gwamanatin Oumar Al-Bashir.
Majalisar Dattawan Amurka ta bude shari’a kan batun tsige shugaban kasa Donald Trump daga mukaminsa, inda Alkalin Alkalan Amurka ya rantsar da yan Majalisar Dattawa masu shari’a, wanda suka yi alkawarin tabbatar da adalci.
Gwamnatin Amurka ta sanya takunkumi akan mataimakin shugaban Sudan ta Kudu na farko Taban Deng Gai, tana mai zargin sa da aikata manyan laifukan keta hakkokin bil Adama da kokarin kawo cikas ga shirin samar da zaman lafiya a kasar da yaki ya daidaita.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce “ga dukkan alamu Iran ta saduda” a jawabin da ya yiwa ‘kasa bayan da makamai masu linzami suka auna sansanonin sojin Amurka biyu a Iraki.
Kakakin Majalisar Wakilan Amurka Nancy Pelosi, ta sanar a jiya Laraba cewa Majalisar za ta kada kuri’a a yau Alhamis da za ta tursasawa shugaba Donald Trump ya gaggauta kawo karshen ayyukan soji akan Iran.
Yanzu dai kimanin makwanni biyu kenan da janye dakarun kasar Chadi daga Najeriya, a dai dai lokacin da hare haren Boko Haram ke kara zafi, lamarin da masu ruwa da tsaki ke bayyana damuwa a kan wannan mataki.
Iyayen ‘yan matan makarantar sakandaren Chibok da suka rage hannun ‘yan ta’addan Boko Haram suna cigaba da kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran mahukuntan Najeriya su taimaka su kwato musu ‘ya’yan su.
Amurka ta kare hare haren da ta kai ta sama a ranar Lahadi da ta auna mayakan da suke samu goyon bayan Iran a Iraqi da Siriya, ta kuma yi gargadin cewa za ta iya sake kai wani harin, duk da irin sukar da jami’an Iran suka yi da kuma wata sabuwar barazana daga mayakan da kan su.
‘Yan kasar Guinea Bissau suna dakon sakamakon zaben shugaban kasar zagaye na biyu, wanda tsoffin Firai Ministan kasar biyu suka fafata kana dukansu sun yi alkawarin dawo da kwanciyar hankali a fagen siyasan kasar.
An gudanar da taron majalisar tsaro ta kasa a Najeriya, inda aka yi nazarin sha'anin tsaro a kasar tare da yanke shawarar fara janye sojoji daga wasu yankunan arewa maso gabashin kasar.
Sabuwsr gwamnatin jihar Zamfara ta jam'iyyar PDP na shirin gurfanar da kimanin mutum 200 gaban kotu don zargin su da bin barauniyar hanya su na karbar albashi.
Ma'aikatar Tsaron Faransa ta ce ta kai wani hari na farko da jirgi mara matuki, da ya hallaka masu tsats-tsauran ra’ayin addinin Islama 7 a tsakiyar Mali a karshen makon da ya gabata.
Dubban ‘yan Iraqi sun gudanar da zanga zanga jiya Litinin a babban birnin kasar Bagadaza da kuma wasu sauran bangarorin kasar, bayan da ‘yan siyasa suka kasa cimma wa’adin da aka debar musu na daren jiya don su bayyana sunan sabon Firai Ministan kasar.
Yayin da ake shirin gudanar da bukukuwan Krismeti da shiga sabuwar shekara wasu garuruwa da birane a arewa maso gabashin Najeriya da aka sha fama da rikice rikicen Boko Haram a baya sun sha kwalliya domin wadannan gagaruman bukukuwa na shekara.
Domin Kari