Kwamitin dattawan arewa da Farfesa Ango Abdullahi ke jagoranta ya gana da masu ruwa da tsaki a Kano, yayin da kwamitin tsohon shugaban Najeriya Janar Abdussalami Abubakar dake kokarin sulhunta takaddamar dake tsakanin gwamna da sarkin Kano ke ci gaba da aikinsa.
Mayakan ‘yan aware na yammacin kasar Kamaru sun sace akalla ‘yan takara 40 da suke takarar majalisa da kananan hukumomi, a wani yunkuri na kawo cikas a zaben da aka tsara za’a gudanar a watan Fabrairu mai zuwa.
Yayin da ake tsammani majalisar wakilan Amurka zata kada kuri’ar tsige shugaba Donald Trump a wannan makon, fadar White House ta maida hankalinta a majalisar dattawan kasar da ‘yan Refublikan ke da rinjaye, inda shugaban kasar zai fuskanci shari’a a farkon watan Janairu.
Kungiyar Tarayyar Turai ta EU, ta shirya wani taro a jihar Adamawa domin duba batutuwan take hakkin mata da kananan yara da kuma hanyoyin da za a bi domin magance irin wannan mummunar dabi’ar.
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya yi kira ga dakarun Najeriya da su gaggauta bude babbar hanyar Maiduguri zuwa Damboa da Biu mai muhimmanci ga tsaro da safarar kayan abinci.
Yanzu haka ana fargabar akalla mutane takwas sun mutu bayan da wani dutse ya barke da aman wuta jiya Litinin da yamma a wani tsibiri da ke arewacin kasar New Zealand, daya daga cikin manyan tsibiran kasar guda biyu. Kana mutane da dama sun jikata.
Hukumomi a kasar Uganda sun ce adadin wadanda suka mutu daga ambaliyar ruwar da kuma zaizayar kasar da aka shafe mako daya ya karu zuwa mutane 36 kana kuma ya bar dubbai a makale bayan da wamakon ruwan ya mamaye yankin da tsaunuka suke.
'Yan jam’iyyar Demokrat da ke jagorancin majalisar wakilan Amurka suna shirye shiryen sanar da daftarin dokar tsige shugaban Amurka Donald Trump da sanyin safiyar yau Talata.
Sashen Hausa na Muryar Amurka ya gudanar da taron zauren VOA da ya saba shirywa a kowane wata a birnin Abuja domin tattaunawa a kan batutuwa da suka shafi rayuwar al’umma da ci gaba kasa da baki dayan zamantakewar jama’a.
Ranar ‘Yancin Dan Adam ta kasa da kasa, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin nazari a kan take hakkin bil adama a duniya. Tun a shekarar 1948 ne aka ayyana ranar goma ga watan Disamban ko wace shekara ranar ‘yancin dan Adam.
Miliyoyin mutane a kudanci da gabashin Afrika na fuskantar karancin abinci da sauyin yanayi ya haddasa, wanda rabinsu yara ne, a cewar kungiyar bada agaji ta Save the Children.
A wannan makon shugaban Amurka Donald Trump zai je birnin London don halartar taron kungiyar tsaro ta NATO, yayin da ake cigaba da takaddamar tsige shi a gida Amurka da ya shiga wani sabon babi.
Ranar uku ga watan Disamban kowace shekara rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin tunawa da wadanda suke da nakasa, kama daga guragu da makafi da kurame da kutare. Wadannan masu lalura suna dogara ne da barace barace domin wajen gudanar da harkokin rayuwar su.
A jiya Litinin shugaban Amurka Donald Trump ya sake bada wani jawabi da ya saba da abinda aka yi na yin canji a shugabancin a ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon.
Shugabar Yankin Hong Kong ta ce zata mutunta sakamakon zaben kananan hukumomi wanda ‘yan takarar masu rajin kare Demokradiyya suka yi gagarumar nasara kuma tace wannan zai kawo sauyi sosai.
Wata kungiya mai goyon bayan shugaban Najeriya dake kiran kanta “Buhari Media Organsation” (BMO), tace shugaba Muhammadu Buhari bai yanke wata shawarar yin tazarce ba
Mata a kasar Zimbabwe suna dogara da unguzomomi ala tilas sakamakon tabarbarewar tsarin kiwon lafiyar kasar kana suna haihuwa a cikin yanayi maras tsabta, lamarin da masana suka ce yana jefa iyaye mata da jariransu a cikin hatsarin kamuwa da cutuka.
Ministan Harkokin Wajen Libya ya fada jiya Litinin cewa harin da aka kai da jirgi mara matuki da ya yi sanadin mutuwar mutane akan kamfanin biskit a Tripoli babban birnin kasar, na iya zama laifin yaki.
Domin Kari