Yau Litinin Yan Jam’iyar Democrat a nan Amurka zasu kadamar da babban taron jamiyar na kwanaki hudu da za’a gudanar ta yanar gizo.
Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a jiya Asabar cewa zai jarraba daukar wani mataki mai tsarkakiya na maido da takunkuman Majalisar Dinkin Duniya a kan Iran, bayan kwamitin sulhun majalisar ya yi watsi da bukatar Washington na kara lokacin haramcin hada hadar makamai a kan Jamhuriyar Islamiya.
Adadin bakin haure da suka isa gabar tekun Italiya sun ninka adadi na bara, yayin da matsalolin tattalin arziki a Tunisia ke kara iza bakin haure a cikin kwale kwale zuwa tekun Maditareniya, inji ministan harkokin cikin gida Luciana Lamorgese a jiya Asabar.
Amurka da kasar Poland sun sanya hannu a kwanan nan a kan tattaunawar inganta yin aiki tare a kan tsaro a jiya Asabar a birnin Warsaw.
Adadin gwajin tabbatar da cutar coronavirus a Amurka a duk rana ta Allah yayi kasa a karon farko, duk da kira sashen kiwon lafiyar jama’a da jami’an tarayya ke yi da a kara yawan gwaje gwaje a Amurka.
Gwamnatin Amurka ta sanar a wannan mako cewa zata fara hana bada biza ga mutanen dake katsalandan ga gwamnatin farar hula ta kasar Sudan. Umarni zai shafi jami’an tsohuwar gwamnatin shugaba Omar al Bashir da aka hambarar da ita da wasu da dama, inji sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo.
A jiya Juma’a, Amurka ta gaza samun daman kara lokacin haramcin harkar makamai da Majalisar Dinkin Duniya(MDD) ta dorawa Iran dake karewa a wannan lokaci, lamarin da ake gani akwai yiwuwar Amurka zata maido da takunkuman kasa da kasa da ta dorawa Tehran.
Yawaitar annobar COVID-19, yasa birane da garuruwa a fadin Amurka suna fama da rashin isasshen haraji, lamarin dake barazana ga katsewar ayyukan bukatun mazauna garuruwan da suka dade suna dogaro a kai.
Kasar Canada ta sanar a jiya Juma’a cewa zata ci gaba da kulle iyakarta da Amurka ga matafiya da basu da muhimmin abin yi zuwa wata na gaba, yayin da Amurka ke ci gaba da zama kasar da tafi yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a duniya da ma yawan wadanda suka mutu da cutar.
Jihohi biyar na Amurka suna gudanar da zabuka a jiya Talata, da ya hada da 'yar majalisa daga jihar Minnesota Ilhan Omar, babbar mai sukar Shugaba Donald Trump, ta fuskantar kalubale mai tsauri a zaben fidda gwani na jam’iyyar Democrat a gundumar Minneapolis.
Dan takarar da ake kyautata zaton shi zai tsayawa jam'iyyar Democrat takara a zaben shugaban kasa Joe Biden, ya zabi Sanata Kamala Harris a matsayin abokiyar takararsa, mace ta farko bakar fata- ba'indiya da wata babbar jami'yya ta taba zaba.
A jiya Talata Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce tana tattaunawa da Rasha game da sabon rigakafin COVID-19 da aka amince dashi kwanan nan.
Fiye da mutane 70 aka kashe, sannan da dama suka jikkata a wata arangamar da ta shafi sojoji da fararen hula a jihar Warrap a Sudan ta Kudu a karshen makon nan, in ji jami'an yankin da jami’an majalisar dinkin duniya.
Shugaban Amurka Donald Trump a jiya Asabar ya bada amincewar sa ga ci gaba da tsarinn nan da ya zo karshe, na bada tallafin ga miliyoyin Amurkawa da suka rasa ayyukan su a lokacin barkewar annobar coronavirus kana ya dakatar harajin albashi.
Kasar Brazil a jiya Asabar ta zo matsayi na biyu a duniya na yawan mace macen coronavirus da mutum dubu dari bayan Amurka, wacce take ta farko da mutum sama da dubu 161 da suka mutu da cutar wacce take kuma da kusan mutum miliyan biyar da aka tabbatar da sun kamu da cutar.
Yawan ruwan ambaliya a yankunan kudancin Somalia ya fidda sama da mutum dubu 650 daga gidajen su a cikin wannan shekara.
Tsibirin Mauritius dake gabar tekun India ya ayyana dokar tabaci a kan muhalli, bayan kwanaki da tan mai yawa na man fetur ya tsiyaye a cikin wani jirgin ruwa mallakar kasar Japan a kan teku.
Domin Kari