‘Yan Nigeria zasu ziyarci rumfunan zabe domin kada kuri’unsu a zaben da aka kasa shi gida uku a cikin wata guda. Bayan zaben ‘yan majalisar dokokin da za’a gudanar Asabar 2 ga watan Afrilu, sai kuma mako na gaba Asabar 9 ga watan Afrilu a gudanar da na shugaban kasa inda shugaba Goodluck Jonathan ke fuskantar takara tare da tsohon shugaban Gwamnatin mulkin sojin Nigeria, janar Muhammadu Buhari. Zagayen zabe na uku kuma shine na ranar Asabar 16 ga watan Afrilu wanda shine zaben Gwamnonin jihohin Nigeria da na ‘yan majalisar jihohi.