Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan ta Kudu: Sojojin 'Yan Tawaye Za Su Hade Da Na Gwamnati


Wasu cikin sojojin 'yan tawaye da za su hade da na gwamnatin Sudan ta Kudu
Wasu cikin sojojin 'yan tawaye da za su hade da na gwamnatin Sudan ta Kudu

Biyo bayan yarjejeniyar zaman lafiya da suka kulla wasu sojojin 'yan tawaye da suka hada da Birgediya Janar Chan Garang

Wani gungun sojojin tawaye na kasar Sudan ta Kudu zai hade da sojojin gwamnatin kasar, wannan ko ya biyo bayan yarjejeniyar samun zaman lafiya da aka kula a watan da ya gabata tsakanin bangarorin ‘yan tawaye da gwamnatin kasar.

Birgediya Janar Chan Garang ya fada wa manema labarai a ranar Talata a Juba cewa shi da wasu sojoji fiye da 300 zasu hade da sojojin gwamnati.

Haka kuma mai magana da yawun sojan kasar Birgediya Janar Lul Ruai Koang ya tabbatar da wannan labari.

Yanzu haka dai ana sa ran jami’an gwamnati da bangaren ‘yan tawayen su sake sa hannu akan wata yarjejeniyar a matsayin ci gaba da kammala wannan yarjejeniyar wanda za a yi karshen wannan satin a Khartoum babban birnin kasar Sudan.

Yarjejeniyar da aka cimmawa a cikin watan jiya wanda ya farfado da shirin samar da zaman lafiya na shekarar 2015 ya kawo raguwar yawan fadace-fadacen da ake samau a kasar ta Sudan ta Kudu.

Sai dai har wayau akwai wasu batutuwan da sassan biyu basu cimma matsaya akan su ba, musali batun bakin iyakokin su da kuma rawar da mataimakan shugaban kasa guda 5 zasu taka a sabuwar gwamnatin hadin kan kasa da za’a kafa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG