Wasu 'yan matan daga Jahar Barno da suka kubuta daga hannayen 'yan kungiyar Boko Haram, sun gana da wasu 'yan majalisar Amurka, inda suka yi bayani kan irin wahalhalu da suka fuskanta.'Yar majalisar Frederica Wilson, wacce take gwagarmayar neman Amurka ta taimakawa wajen kubutar da 'yan matan da har yanzu suke hanun 'yan bindigar, ita ta jagoranci tattaunawar a majalisar dake nan birnin Washington DC, ranar 7 ga watan Maris shekarar 2018.
Hotunan Wasu 'Yan Mata Biyu Da Suka Kubuta Daga Hannayen 'Yan Boko Haram A Majalisar Amurka

9
Wasu 'yan mata biyu da suka kubuta daga hannayen 'yan Boko Haram, yayinda suke ziyara a majalisar dokokin Amurka tare da wasu wakilan majalisa. Sun kuma gana da wakilan sashen Hausa na Muryar Amurka, Grace Alheri Abdu, tare da Abdoulaziz Adili Toro, Maris 7 shekarar 2018
Facebook Forum