WASHINGTON, D. C. - Hotuna daga kamarar yanar gizo sun nuna yadda wuta ke tashi daga ranin da ke tsakiyar dutsen kuma aman dake fitowa yana kwarara ya mamaye zagayen dusten.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Hawaii ta rubuta a dandalin sada zumunta na Twitter, cewa,aman dutsen "bai haifar da barazana ga al'ummomi ba" ko da yake barbashin wutar da gurbataccen iska na iya haifar da matsalolin numfashi ga mutane idan suka shaka.
Aman dutsen ya kasance gabanin wani lokaci na girgizar kasa mai karfi da kuma "dagewarsa cikin sauri", a cewar USGS. Hukumar ta daukaka lambar launin barazanar ta Kilauea daga kalar lemu wato mai sauki zuwa ja, mai tsanani yayin da take kimanta fashewar ta dutsen mai aman wuta daga yanayin sa ido akai, zuwa gargadi.
Dutsen Kilauea dake cikin wani rufaffen wurin shakatawa na Volcanoes National Park, yana daya daga cikin duwatsu mafi yawan aman wuta a duniya. A cikin shekarar 2019, yawan girgizar dutsen da aman wuta akai-akai ya haifar da lalata ɗaruruwan gidaje da dakatar da kasuwanci.
Dutsen dai ya barke da aman wuta a watan Janairu da Yuni da kuma yanzu Satumba na wannan shekara.
-Reuters
Dandalin Mu Tattauna