Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Bada Gudummawar Dala Miliyan 20 Domin 'Yan Gudun Hijiran Fallujah


Sojojin Iraqi suna taimakawa mutanen dake arcewa daga Fallujah, Iraqi.
Sojojin Iraqi suna taimakawa mutanen dake arcewa daga Fallujah, Iraqi.

Gwamnatin kasar Amurka ta fada jiya Talata cewa zata bada gudunmowar dala miliyan 20 domin aikin jin kai ga ayyukan Majalisar Dinkin Duniya ko MDD, na taimakawa dubban ‘yan gudun hijira da suka bar birnin Fallujah dake cikin kasar Iraqi.

A cikin satin data gabata ne dai sojojin Iraqi suka sake kwato birnin Fallujah daga kungiyar ISIS, da ta rike da birnin har na tsawon shekaru biyu.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta kiyasta cewa kusan mazauna wannan birnin na Fallujah da yawan su yakai dubu 85 suka bar matsugunnin su zuwa cikin babban birnin kasar wato Bagadaza, kuma wadannan bayin ALLAH na bukatar taimako yanzu haka.

Sai dai kwamitin bada agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya aa bada dala miliyan 17 da rabi a ranar Littini domin taimakon wadannan mutanen.

Amurka tace wannan gudummawar data ce zata bayar yana daga cikin taimakon jin kai data kudiri aniyar bayar wa cikin wannan shekarar. Tace ‘yan kasar Iraqi sama da miliyan 3 aka tilasta musu zagaye cikin kasar tun a cikin shekarar 2014 domin gudun kar ayi fada.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG