A cigaba da aikata ta'asa da miyagu ke yi a fadin Najeriya, sun kai wani hari a Nasarawa, inda ake zargin sun sace mutane wajen ashirin, adadin da 'yan sanda ke tababa a kai.
A ci gaba da gabatar da korafe korafe da 'yan Najeriya ke yigaban kwamitin binciken zargin cin zarafi da ake ma rusassshiyar rundunar 'yan sandan musamman ta SARS a fadin Najeriya, a jahar Filato, kwamitin ya fara jin wasu zarge zarge masu tayar da hankali
Kungiyoyin ma’aikatan kananan hukumomin jihar Filato sun fada wani sabon zanga-zanga don jan hankalin gwamnati ta biya su albashi mafi karanci na Naira dubu talatin.
Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta ce tana kan bincike don gano wadanda suka kashe shugaban jam'iyyar APC a jihar, Mista Philip Tatari Shekwo.
Kwamitin shari’a da gwamnatin jahar Filato ta kafa don duba korafin cin zarafi da ake zargin jami’an tsaro da aiwatarwa kan fararen hula, ya ce ya zuwa yanzu ya karbi korafe-korafe guda arba’in da biyar.
Kungiyar mata lauyoyi reshen jahar Pilato ta ce za ta jajirce don ganin an kawo karshen cin zarafin mata da yara a Najeriya.
Tsangwama da ake nunawa mata masu cutar yoyon fitsari na haifar da koma baya ga zamantakewar iyalai.
Biyo bayan zanga zangar #ENDSARS data rikide ta zama tashin hankali, matasa suka shiga wawashe rumbunan ajiyan kayan abinci na gwamnati da kwashe wasu kayan aiki a ofisoshin gwamnati, shugabannan al’umma da na addinai sunyi huduba ga matasan da su kasance nagari.
Matasa a wasu jihohin Najeriya, sun yi ta afkawa rumbunan adand abincin tallafin da gwamnati ta tanada don ragewa mutane radadin annobar coronavirus da ta addabi duniya.
Wata hatsaniya da ta tashi a titin Ahmadu Bello Way daura da Kasuwar Terminus a tsakiyar birnin Jos hedikwatar jihar Filato da ke Arewa ta Tsakiyar Najeriya tayi sanadin rasa dukiyoyi.
Gwamnatin jihar Pilato ta saka dokar hana fita na tsawon sa’o’i 24 a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta kudu, har sai yadda hali ya yi.
Ana ci gaba da zanga zangar nuna kin jinin kuntatawa al’umma da jami’an ‘yan sanda suke yi a birane da dama a Najeriya.
A cigaba da rigimar da ta biyo bayan wasu kalaman da tsohon Mataimakin Babban Bankin Najeriya, Dr. Obadiah Mailafiya ya yi game da matsalar tsaro a Kudancin Kaduna, wata kotu a Jos ta tabbatar da hurumin hukumar 'yan sandan da ta gayyace shi
Jihar Nasarawa ta fara fuskantar barnar ruwa yayinda hukumomi ke fadakar da al’umma kan barazanar da ambaliya ka iya haddasawa a wassu jihohin Najeriya.
A makon jiya ne dakarun da ke wanzadda zaman lafiya suka hallaka Terwase Akwaza wanda ake yi wa lakabi da Gana, a jihar Binuwai, lamarin da sam bai yi wa gwamnan jihar dadi ba.
Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya ce matakan da gwamnati ta dauka zasu magance mafi yawan matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.
Gwamnatin jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar Najriya ta ce a yanzu jahar tana da wuraren gwajin cutar korona guda uku wanda a kullum ke gwada mutum dari hudu da tamanin da biyar.
Domin Kari