Mata ‘yan gudun hijira Musulmai da Kirista dubu biyu da dari biyar sun anfana da tallafin abinci albarkacin bukin Kirismeti a Yola fadar jahar Adamawa.
Hukumomin tsaro a jahar Adamawa sun fara daukar matakan tsaro don tabbatar da ganin anyi bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara lafiya.
A yayin da ya rage kwanaki biyu a gudanar da bikin kirsimeti jama’a na kokawa game da tsadar rayuwa lamarin da kuma zai shafi hidimar ta bana.
Rasha tana makokin jakadenta na kasar Turkiya da aka kashe, a wani shiri da ma’aikatar harkokin kasashen ketare ya shirya a birnin Moscow yau Alhamis.
Alkaluman hukumar lafiya ta duniya da kuma gwamnatin Najeriya na nuni da cewa, farashin magunguna a Najeriya ya ninka na kasashen duniya da dama.
Masana sun bayyana ra’yoyinsu game da sabuwar manufar gwamnatin tarayyar Najeriya, akan bada tukwici ga duk ‘dan Najeriya da ya bada bayanan sirri da akayi amfani da su wajen kwato kudaden da aka sace daga gwamnati.
Hukumar ‘yan sandan jahar Bauchi ta gabatar da wasu mutane sama da ashirin da suka hada da mutumin dake jigilar abinci da kayyakin sa maye wa wata kungiyar masu satar mutane suyi garkuwa da su don kudin fansa.
Bayan da hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama wasu buhunan shinkafar roba, yanzu haka ta sake kama tabar wiwi da kudinsu ya kai Naira Miliyan 250.
Bangarorin PDP biyu na zargin juna da kafa wata sabuwar jam’iyya mai taken MEGA Party da zata fafata da APC a babban zaben Najeriya na shekara ta 2019.
Wata gaguramar wuta ta tashi a wata mashahuriyar kasuwar saida kayan wasan hasken wuta ko kuma fireworks a turance, a kusa da Birnin Mexico inda tayi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 31, 70 kuma suka raunata.
Rundunar tsaro a jahar Filato tace ta ‘dauki matakan tabbatar da gudanar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara lafiya.
A yau laraba Hukumomi a kasar Jamus suka ci gaba da farautar mutumin da ya tuka motar a kori kura cikin wata kasuwa Kasuwar sayar da kayan Kirsimeti dake cike da jama'a a birnin Berlin, kwana daya bayan sakin wani mutum da aka kama, ba da dadewa ba bayan kai wani hari da ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane 12.
Jami’an ‘yan sandan jahar Adamawa sun horas da matasa ‘yan aikin sa kai na ‘yan Banga 251, domin samun dabarun aiki da bayanai a cikin al’umma.
Domin Kari