Kasar Kamaru ta ce wasu ‘yan kalilan ne kawai daga cikin ‘yan gudun hijirar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dinnan 285,000 su ka amince su koma kasarsu.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yiwa Iran kashedi “tayi hankali” bayan ta fada a jiya Lahadi cewa zata kara inganta sinadarin uranium dinta fiye da abin da aka kayyade mata a cikin yarjejeniyar nukiliya a shekarar 2015
Afrika tana shirin shiga wata yarjejeniyar da ta kira ta zaman lafiya da ci gaba ta hanyar kulla yarjejeniyar kasuwanci a nahiyar a hukumance.
Shugabanin kasashe da na gwamnatocin nahiyar Afirka sun bayyana ranar 7 ga watan yulin 2020 a matsayin ranar fara aiki da yarjejeniyar cire shingayen dake tsakainin kasashe don baiwa jama’ar nahiyar damar gudanar da harkokin kasuwanci ba tare da wata tsangwama ba.
Kamar yadda masana ke cewa matsalar tsaro ita ke kan gaba wajen hana ci gaban kasa, kama daga tashe tashen hankula dake da nasaba da fadan kabilanci ko na addini, zuwa ga matsalar yan ta'adda kai har zuwa ga batun yan jagaliya.
Gabannin fara jigilar alhazan Najeriya zuwa Saudiyya a Larabar nan, hukumar alhazan NAHCON ta gargadi alhazai su yi takatsantsan da duk abin da za su shiga da shi Saudiyya don kar wasu su yi musu sakiyar da ba ruwa.
Da safiyar jiya Alhamis ne aka samu girgizar kasa mai girman maki 6.4 a kudancin jihar California, lamarin da ya haifarwa dubban gidaje a yankin rasa wutar lantarki har ma da gobara.
Bakin haure 83 daga nahiyar Afirka sun mutu, wasu uku sun tsira da ransu lokacin da jirgin ruwansu ya nutse kwanaki biyu da suka gabata, a gabar tekun Tunisia, a cewar dogarawan teku.
Kungiyar kula da bakin haure ta kasa da kasa (IOM a takaice), ta ce bakin haure sama da 32,000 ne su ka mutu ko su ka bace bat a fadin duniya tsakanin 2014 da 2018, kuma an fi samun mace-macen bakin hauren ne a yayin ratsa tekun Bahar Rum mai cike da hadari, don a je Turai daga Arewacin Afirka.
Shugaba Donald Trump ya zama shugaban Amurka na farko da ya kai ziyara a Korea ta Arewa, inda ya taka ya tsallaka iyakar kasar, a lokacin da suke ganawa da shugaban korea ta Arewa Kim Jong Un a yankin da ba a gudanar da ayyukan soji.
Jami’iyar adawa a Trukiya tayi gagarumar nasara a zaben magajin birnin Istanbul mai tattare da matsaloli. Wannan nasara wata babbar koma baya ce ga shugaban kasar Racep Tayyip Erdogan wanda ya sha kashi a Istanbul da ake ganin yafi tasiri tsawon shekaru 25.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce baya neman yaki da kasar Iran kuma yana niyar tattaunawa da shugabanninta ba tare da wasu sharuda ba, amma kuma ya ce ba za a kyaleta ta ci gaba kera makaman kare dangi na nukiliya ba.
Rahotanni daga garin Oyibo dake jihar Rivers na nuni da cewa akalla mutane tara ne suka rasa rayukansu, sakamakon fashewar wani bututun Mai mallakar kamfanin Mai na Shell a yankin Niger-Delta.
Saura kiris Amurka da Iran su gwabza jiya Alhamis bayan da aka kakkabo jirgin sintirin Amurka mara matuki mai suna Global Hawk a yankin ruwan Hormuz, al'amarin da Shugaban Amurka Donald Trump ya kira "mummunan kuskure."
Sa'o’i kadan da babbar kotun Kaduna ta yanke hukuncin cewa kudurin dokar kula da wa'azi a Kaduna ya sabawa dokar ‘kasa, wasu shugabannin addini sun ce da ma sun san za a rina.
Hukumomin tsaro a jamhuriyar Nijer Sun sanar cewa dakarun kasar da hadin gwiwar takwarorinsu na kasar Amurka da na rundunar Barkhane sun karkashe wasu gaggan 'yan ta'addan reshen kungiyar IS a Sahara.
Domin Kari