Hukumar raya kasashe masu tasowa ta kasar Amurka USAID a takaice, zata fadada ayyukan kungiyar samar da zaman lafiya ta kungiyar mata ta WOWWI zuwa kasar Nijar.
Hedikwatar kungiyar Kwadago ta Najeriya zata tare a jihar Imo da nufin sa kafar wando daya da gwamnatin jihar, bayan korar ma’aikata sama da dubu uku.
Yanzu haka dai masana harkar shari’a da kuma kungiyoyin kare hakkin Dan Adam a Najeriya, na ci gaba da maida martani game da kalaman da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yayi na cewa alkalai ne ke zama kandagarki na kokarin yaki da cin hanci da gwamnatinsa ke kokari a yanzu.
Rotanni da ke fitowa daga jihar Borno na nuna da cewa rundunar sojan Najeriya sun sami nasarar hallaka wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne, har fiye da 100 a wani sumame da ta kai kan wasu ‘kauyuka.
Yanzu haka dai garin damagaran ya dauki harama tun da aka gudanar da yakin neman zabe a hukumance, komai ya kankama inda jam’iyyu suka lika fastoci da kyallaye a tituna da jikin motocinsu.
Rundunar sojin Najeriya ta kare matakin da ta dauka na sake maida tsohon kwamandan yaki da Boko Haram, Janar Ahmadu Mohammed bakin aiki bayan da kungiyar rajin kare ‘yan cin Bil Adama ta Amnesty International ta zargeshi da karkashe fararen hula a Arewa maso Gabashin Najeriya.
Shari’un zaben shekara ta 2015 na gwamnoni na samun hukunci ba tare da jinkiri ba a kotun koli, inda gwamna Gaidam na Yobe ya samu nasara kan karar da ‘dan takarar PDP Adamu Maina Waziri ya shigar yana zargin tafka magudi a zaben.
Hukumar lafiya ta duniya wato WHO a turance tace ta ayyana dokar ta baci game da cutar nan ta zika dake yaduwa kamar wutar daji.
Bayan kwashe kwanaki ana rigima tsakanin Fulani makiyaya da Manoma a kauyuka hudu na karamar hukumar Girei dake Adamawa, da ya haddasa asarar rayukan mutane da dama.
Tsohon gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya musanta rahotannin da wasu jaridun Najeriya suka wallafa a karshen makon jiya.
Yanzu haka dai dan takarar shugaban kasa a karkashin tutar jamiyyar Republican Ted Cruz, shine ya lashe zaben fidda gwani wanda akayi a jihar Iowa, inda ya doke abokin karawarsa Attajirin nan Donald Trump.
Jihar Niger dake Arewa maso tsakiyar Najeriya, ta cika shekaru 40 da zama ‘daya daga cikin jihohin Najeriya. A shekarar 1976 ne shugaban mulkin soja na wancan lokaci ya marigayi Murtala Ramat Muhammad, ya cire jihar Niger daga tsohuwar jihar Sokoto dake Arewa maso Yammacin Najeriya.
Hukumar bada tallafi ta Amurka ta sanar da bada tallafin makudan kudin agajin da suka kai Dala Miliyan 97 a matsayin daukin gaggawa ga kasar Ethiopia na matsalar masifar da kan shafi bil’adama da suke fuskanta na dumamar tekun da ake cewa El’Nino.
Wasu kwararrun a fannin lafiya suna hasashen cewa cutar nan ta ZIKA da ta bullo daga Kudancin Amurka na iya zama barazana ga lafiyar duniya fiye da cutar Ebola da ta kashe mutane fiye da 11,000 a kasashen Afirka.
‘Yan Boko Haram sun kai hari a wani kauye inda suka kashe akalla mutane 50. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa, ‘yan ta’addar sun dirarwa kauyen Dolari da daddaren ranar Asabar suka dinga harbin jama’a tare da kona gidaje.
Taron kungiyar kasashen Afirka ya tashi bisa yarjejeniyar jingine maganar fasa kai rundunar sojin kiyaye zaman lafiya a kasar Burundi mai fama da rikici.
Sakataren watsa labarai na Jam’iyar PDP mai adawa Olisa Metuh, ya ce yawan kararraki da ake shigar wa da hukunce hukuncen da Kotuna ke yankewa kan ‘ya'yan jamiyyar yana nunin Jam’iyyar tana nan da karfin ta har ma za ta iya karban mulki a shekara 2019.
Kungiyar masu gasa Buredi da ke jihar Borno, zasu dakatar da gasa Buredi har na tsawon kwanaki uku, a wani mataki na nunawa gwamnati irin matsalolin da suka shiga, musammam ma na tsadar kayayyakin gasa Buredin.
A farkon fara yakin neman zaben shugaban kasa hade da na ‘yan majalisun dokoki a kasar jamhuriyar Nijar, galibin cibiyoyin jam’iyyun siyasa sun fara gargadin matasa da su kiyaye tsokano tashin hankali domin gudanar da zabubbuka cikin lafiya da kwanciyar hankali.
Domin Kari