Manyan jami'an Diplomasiyya biyu na Amurka sun zargi kasar Rwanda da bada gudunmawar ta wajen ganin makwabciyar ta Burundi naci gaba kara wargajewa.
Gwamnatin tarayyar Najeriya tace zata kara tsaurara matakan tsaro a sansanin ‘yan gudu hijira. Bayan da wasu ‘yan kunar bakin wake su biyu suka tada bomb a sansanin dake Dikwa, wanda yayi musabbabin mutuwar ’yangudun hijra har su 58.
Majalisar Koli ta Jam’iyyar PDP za tayi taro ranar Talata mai zuwa domin tattaunawa kan matsayin shugaban jam’iyyar, domin maye gurbin Adamu Mu’azu daga shiyyar Arewa maso Gabas. A cewar Sanata Walid Jibrin a wata hira da wakilin Muryar Amurka.
Rahotanni daga jihar Taraba Arewa maso Gabashin Najeriya, na cewa awa 74 bayan sace mahaifiyar mataimakin gwamnan jihar Haruna Manu da wasu yan bindiga suka yi a garin Mutum Biyu, yanzu haka ta samu kubuta daga hannun wadanda ke garkuwa da ita.
Rahoanni daga jihar Adamawa Arewa maso Gabashin Najeriya, na cewa wasu yan bindiga da ake kyautata zaton cewa yan Boko Haram ne sun sake kai wani hari akan wasu kauyuka dake kan iyakar Najeriya da Kamaru, ta yankin Madagali.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta maida martani ga Sanata Baba Kaka Bashir Garbai kan kalamansa na cewa yan Boko Haram har yanzu suna rike da galibin sassan jihar Borno.
Gwamnatin Najeriya a karon farko ta bayyana matsayinta dangane da karin kudin wuta da ya janyo zanga zangar gama gari a ko ina cikin kasar.
Ana kyautata zaton a yau Laraba ‘Yan Majalisar Dokokin Amurka zasu rattaba hannu akan amincewa da gagarumin takunkumi akan kasar Koriya ta Arewa, ‘yan kwanaki kadan bayan gwamantin ta Pyongyang ta gwada harba rokar da ka iya dakon makamin Nukiliya mai cin dogon zango, wanda ‘yan makonni ne tsakanin wani gwajin Nukiliyar da ta yi.
Dan siyasar mai ra’ayin sassauci na jam’iyyar Democrat Sanata Bernie Sanders da kuma dan baro-baro Donald Trump na jam’iyyar Republican da suke neman shugabancin Amurka, sun sami lashe zaben fidda gwanin da aka yi a New Hamshire bayan gama na Iowa a makon da ya gabata.
A jiya Talata, Shugaban kasar Chadi Idriss Deby yace zai tsaya takarar shugabancin kasar karo na 5 a zaben da ke tafe a watan Afrilun shekarar nan, inda yayi alkawarin dawo da iyakar wa’adin mulki matukar ya ci zaben.
Labarin kama wanda ake zargi Abdussalam Enesi Yunusa, da laifin aikin horas da yan Najeriya su shiga kungiyar ta’addanci ta ISIS da ‘yan Sandan Asiri DSS na Najeriya suka yi na nuna fadadar aikin ta’addanci fiye da Boko Haram a kasar.
Mata sunyi gangamin yaki da al’adar yiwa mata kaciya cikin sabon yunkurin kawo karshen al’adar da kan yiwa mata illar din din din.
Yanzu haka dai kusoshin kungiyar Kwadago ta Najeriya sun tattaru a jihar Imo da nufin yiwa gwamnatin jihar taron dangi.
Komitocin da ke Kula da kasafin kudi a Majalisar dokokin Najeriya, sun ce akwai kura kurai dayawa a kasafin kudin bana.
Kamar yadda rahotanni ke nunawa zuwa yanzu ba’a ceto mahaifiyar mataimakin gwamnan jihar Taraba,Haruna Manu da wasu yan bindiga suka sace a garin mutum biyu,wanda yanzu haka ba’a san halin da take ciki ba.
A kalla mutane 12 ne suka mutu wasu da dama suka samu rauni daban-daban a gabashin kasar Jamhuriyar Demokaradiyyar Kongo. Inda a cikin ‘yan makonnin nan ya kasance cikin matsanancin mummunar fadar kabilanci.
Rahotanni daga jihar Taraba Arewa maso Gabashin Najeriya, na cewa wasu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba, sun sace mahaifiyar mataimakin gwamnan jihar Taraba, Hon. Haruna Manu.
Majilisar Dinkin Duniya tayi gargadi a jiya litini cewa za a samu matsanancin karancin abinci a kasar Sudan ta Kudu, wanda hakan zai tura dubun dubatar ‘yan kasar cikin halin kaka ni kayi na rashi abinci musammam ma fafaren hula.
Domin Kari