Yanzu haka dai ana cigaba da cecekuce a tsakanin gwamnatin PDP da kuma bangaren yan hamayya a jihar Taraba, inda gwamnan jihar Darius Dickson Isiyaku, ke kokarin hada kan al'ummar jihar ta hanyar kafa gwamnatin kowa da kowa, yayin da bangaren APC ke cewa an yi mata kwace.
Kimanin ma’aikatan bogi 600 ne gwamnatin jihar Neja tace ta bankado a wani binciken kwa kwaf da gwamnatin jihar ke yiwa ma’aikatanta a halin yanzu.
Gwamnan jihar Yobe yayi bayani game da matsalolin da jihar ta fada, dama matsalar tattalin arziki da jihar tabi sahu kamar sauran jihohi dama gwamnatin Tarayya suke kuka akai, dakuma sama da fadi da yace wasu ma’aikata nayi wanda aka fara gano su.
Rundunar Tsaro ta Special Task Force (STF) a jihar Plateau, ta cafke mutane 8 da take zargi da hannu wajen rikici tsakanin kabilar Berom da Irigwe a karamar hukumar Bassa dake jihar.
Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC Ibrahim Magu, ya fara shiga kafar wando daya da wadansu manyan lauyoyi masu zaman kansu, a kokarin da yake yi na warware tarnaki da zagon kasa da yake zargin suna yiwa aikin hukumar EFCC.
Cincirindon ma’aikatan jinya na kananan hukumomi 21 a jihar Adamawa, sun gudanar da wata zanga zangar lumana domin nuna fushinsu game da rashin biyansu albashin na wasu watanni.
Wannan shine karon farko a wannan shekara da rundunar ‘yan Sandan jihar Zamafara, ta sami gagarumar nasara, a yakin da take yi da ‘yan bindagar da ke kai hare hare a wasu yankunan jihar inda suke karkashe mutane tare da yin awon gaba da Shanunsu.
Shahararriyar ‘yar siyasar nan Hajiya Naja’atu Muhammad, tayi karin bayani kan dalilan da yasa taki karbar mukamin da gamnatin Tarayya ta bata.
A zaman da Majalisar Dattawa ta yi a jiya Talata ta yanke hukuncin soke Karin kudin Wutar lantarki da Hukumar Kula da Kamfanonin bada wuta suka yi.
Bincike na nuni da cewar kimanin mutane biyu ne ke mutuwa a cikin kwanaki uku, a kauyukan Goldimare da kuma Iyadema a karamar hukumar Shongom dake jihar Gombe, a sanadiyar cizon macizai.
Jami’an Majalisar Koli ta Jam’iyyar PDP sun share wuni guda domin zaben shugaban jam’iyyar daga Arewa maso Gabas, inda daga karshe tsohon gwamnan Borno Ali Modu Sherif, ya zamanto shugaban Jam’iyyar.
A wani yunkuri na magance hare-haren kunar bakin wake da yanzu ake kaiwa a sansanonin yan gudun hijira, yanzu haka an kara tsaurara matakan tsaro a sansanonin, yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke kokarin kawo karshen kungiyar Boko Haram.
Jami’an tsaron farin kaya na Civil Defense dake jihar Borno, sun gurfanar da wani mutum mai shekaru 50 ga manema labarai da suka ce sun kama shi yana sayar da form din jabu ga ‘yan gudun hijira dake garin Maiduguri, da sunan za a kawo musu tallafi daga Abuja.
A wani taron manema labarai Kwamishinan Kiwon Lafiya na jihar Ogun, Dr. Babatunde Efayena, ya sanar da cewa matar nan ta farko da ta kamu da zazzabin Lassa a jihar Ogun ta rasu, haka kuma wata ta biyu ta kamu.
A yayin da kwamnitin da gwamnatin jihar Kaduna ta kafa domin binciko musabbabin hayaniyar da ta tashi tsakanin mabiya darikar Shi’a a Zariya, da kuma rundunar sojan tarayyar Najeriya dake Kaduna. Wata kungiyar mata mabiya masahabar Shi’a tayi zanga zangar nuna damuwa a garin Kaduna.
Kwararru akan fannin gona a Najeriya sun fara bayyana ra’ayinsu tare da nuna mafita akan tashin farashin kayan abinci a kasar.
Rahotanni daga jihar Taraba Arewa maso Gabashin Najeriya, na cewa wasu dauke da mugayen makamai sun kai hari a yankin Damfar na karamar hukumar Ibi, inda aka samu asarar rayuka.
Domin Kari