Shugabar Asusun Lamuni na Duniya (IMF), Christine Lagarde, ta fadi yau Talata cewa ya kamata duniya ta hada kai don shawo kan kalubalolin tattalin arziki, ciki har da tafiyar hawainiya da tattalin arziki ke yi, da faduwar farashin kaya da kuma tsuke bakin aljuhun da gwamnatoci da dama ka yi nan gaba.