Yau ce ranar kula da koshin lafiyar ma’aikata a wuraren ayyukan su da kuma basu kariya daga kowace barazana, yayin da suke bakin aiki. Kungiyar kwadago ta duniya ce ta ware kowace ranar 28 ga watan Afrilu domin gudanar gangamin wayar da kai dangane da muhimmancin ranar.
Hukumomin tsaron Najeriya da na jamhuriyar Nijar na ci gaba da kara tuntubar juna domin bullo da sabbin matakan tunkarar kungiyar Boko Haram, baya ga matakan cikin gida da kowace kasa ke dauka anata bangare domin murkushe hare haren ta’addancin wannan kungiya.
Shiyyar Kano ta kugiyar dillalan Man fetur masu zaman kansu ta umarci ‘yayan kungiyar su daina sayo Mai daga hannun ‘yan kasuwa domin sayarwa ga masu ababen hawa a jihar Kano.
Rikici da kuma zarge zargin cewa, jam’iya mai mulki na tace labarai, sun kawo koma baya a lokacin da ya kamata a gudanar da bukuwa a kasar Tanzania dake kudancin Afrika.
Madugun ‘yan tawayen kasar Sudan ta Kudu Reik Machar ya koma babban birnin kasar Juba, wani muhimmin matakin da ya yiwu, ya kawo karshen yakin basasan da ake yi a kasar.
Yayin da gwamnatin Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ke cika shekara guda a watan mayu na gobe, Jam’iyyar Hamayya ta PDP tana daukar matakan kwace madafun iko a shekara ta 2019. Hakan dai na daga cikin kalaman shugaban PDP na kasa Sanata Ali Modu Sheriff lokacin daya ke jawabi ga ‘yayan Jam’iyyar jiya a Dutse jihar Jiagwa.
A yayin da ‘ya’yan jam’iyar PDP ta adawa a Najeriya ke cigaba da caccakar jam’iyyar APC mai mulki da rashIn shawo kan matsalar tattalin arziki da yawancin yan kasar ke kukan matsanancin hali da suke fuskanta tun hawan gwamnatin shugaba Buhari.
Amurka ta yanke shawarar karbar wani matsayi na bayan- fage, a yunkurin sasanta rikicin Sudan ta Kudu da ake yi tsakanin gwamnatin kasar da ‘yan tawaye, bayan cikas da aka samu wajen kafa gwamnatin hadaka a tsakanin bangarorin biyu.
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce, nan da shekaru hudu masu zuwa, wasu kasashen Afrika za su kawar da cutar cizon sauro ko kuma Malaria.
Gwamnatin jihar Oyo zata hana bara akan tituna tare da kama Almajirai domin gabatar da su gaban Shari’a.
Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC, ta fara yin nazari kan wasu rahotannin zargin aikata laifukan kisa da azabatarwa da fyade, sanadiyar rikicin siyasar kasar Burundi.
Yanzu haka wata sabuwa ta kunno kai game da batun zaben kananan hukumomin jihar Adamawa 21, inda ake yunkurin sauya jadawalin gudanar da zaben, haka yasa jam'iyyun ke cewa ba zata sabu ba wai bindiga a ruwa.
Gwamnatin Tarayyar Najeriya karkashin jagorancin shugaba Mohammadu Buhari, ta dagawa gwamnonin jihohi kafa dangane da fara biyan basussukan da aka basu, daga wannan wata zuwa wata na sama.
Shugaban kasar Chadi Idris Deby ya lashe sabon wa’adi wanda wannan shine karo na biyar, a kan karagar mulki. Deby ya buge abokan karawar sa har su 13 da gagarumar tazara, sai dai ‘yan adawar sun zarge shi da tafka magudi a zaben.
Ba sabon labari bane yadda duk wani gwamna da ya kammala wa’adin mulki karo na biyu a Najeriya, kan nemi takarar tafiya Majalisar Dattawa, inda yawancin tsofaffin gwamnonin kanyi amfani da tasirinsu wajen lashe zabe.
Hedikwatar tsaron Najeriya ta fitar da wata sanarwa dake ankarar da jama’a kan yadda ‘yan ta’addar Najeria ke jan hankalin matasa ta hanyar basu lamani, kuma wannan tsari na gudana ne musamman a Arewa maso Gabas.
A yau anyi wata ganawa ta musammam tsakanin shugaban Najeriya Mohammadu Buhari da jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power.
Domin Kari