Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta sanar yau Talata cewa, sama da bakin aure dubu biyu da dari biyar ne, ciki har da 'yan Nigeria, suka rasa rayukansu yayinda suke kokarin ketara tekun Baharam zuwa kasashen turai kawo yanzu a shekara ta dubu biyu da goma sha shida.