Wani rahoto ya nuna cewa, Amurka na cigaba da zama kasar da ta fi kowace sayar da makamai a duniya, inda ta samu kusan dala biliyan 23 daga makaman da ta sayarwa kasashe a shekarar da ta gabata, musamman kasashen da ke Gabas ta Tsakiya.
Manyan jam’iyun adawa a Jamhuriyar Dimokradiyar Congo, sun bayyana cewa sun dunkule a karkashin lema daya.
Hadakar kungiyar malamai ta Najeriya, NUT, ta nuna fushinta game da rashin biyan albashi na malaman makarantun firamare a jihar na tsawon watanni, lamarin da yasa malaman fusata da rufe makarantu, yanayin da yasa dalibai komawa gida.
Yau ce ranar gangamin wayar da kan Jama’a kan bukatar mutunta mutane masu lalurar fata wato Zabiya da kuma kare su daga dukkan wani nau’i na cin zarafi ko muzgunawa a sassan duniya.
Yarjejeniyar dawo da ‘yan gudun hijirar Najeriya kimannin Dubu 80 na nuna yawan ‘yan Najeriya da suka tsallaka ketare, domin tsira da ransu sakamakon futunar Boko Haram.
Hukumomi a gabashin garin Nangarhar da ke Afghanistan, sun ce wani bam da ya tashi a lokacin ana salla ya kashe akalla mutane hudu, sannan ya raunata wasu da dama.
Dubun dubatar mutane ne ake sa ran za su jeru a gefen titunan garin Musulmin farko da ya fi shahara a Amurka, domin yin ban kwana da gwarzon dambe Muhammadi Ali, wanda ya rasu a ranar juma’ar da ta gabata yana mai shekaru 74.
Kungiyar Kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta ce sojojin Najeriya sun kashe akalla mutane 17 a lokacin wani gangami da ‘yan awaren kungiyar Biafra suka yi a kudu maso gabashin kasar.
Hukumar kwastan mai yaki da fasa kwauri ta kama miyagun kwayoyi nau’in tabar wiwi na kusan Naira Miliyan 400 a cikin watanni shida na wannan shekarar, wanda ake niyyar shigowa dasu Najeriya.
A jihar Gombe hukumar gudanarwar kwalejin ilmi ta gwamnatin tarayya, ta rufe kwalejin har sai abin da hali yayi.
Tsohuwar sakatariyar ma’aikatar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta shiga tarihi, a matsayin macen farko da za a tsayar takarar shugaban kasa karkashin manyan jam’iyun siyasar kasar biyu.
Domin Kari