Duk da irin maida hankali da kuma kudade da ake warewa a Amurka da sauran kasashen duniya domin yaki da ayyukan ta’addanci, kisan kiyashin da ya auku ranar Lahadi a Orlando da ke jihar Florida, ya nuna cewa harin da daidaikun mutane ke kaiwa, ya zama babban kalubale ga gwamnatoci.