A yau Litinin, Ministan harkokin cikin gida na kasar Sa’udiyya yace, wani dan kunar bakin wake ya tada kansa da bom a kusa da ofishin Jakadancin Amurka da ke birnin yammaci na Jeddah.
Firayim Minista Isra’ila Benjamin Netenyahu yana kasar Uganda, a wata ziyarar da ba kasafai akan yita ba zuwa kasashen yankin saharar Afirka, ziyarar da ya fara don tunawa da wani ceton wadansu da aka taba garkuwa da su a shekarar 1976.
A karo na hudu kungiyar Izala reshen jihar Oyo, ta rarraba kudade sama da Naira Miliyan 3 da turaman atamfa da yaduna ga marayu da zawarawa da gajiyayyu.
A yau Litinin ne Amurka ke bikin cika shekaru 240 da samun ‘yancin kai daga kasar Birtanijya. Inda a rana irin ta yau 4 ga watan Yuli ake bada hutu a duk fadin kasar, tare da yin shagulgula, da fareti tare harba tartsatsin wutar murna a sama.
Gwamnatin Najeriya tace duk da irin hare haren da ‘yan kungiyar Avengers ta Niger Delta ke kaiwa a tashoshin man Fetur a yankin, tace zata ci gaba da nemo hanyar sasantawa domin kawo karshen wannna matsala.
Kotun kolin kasar Austria ta yanke hukunci a yau Juma’a na soke zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Mayu, bayan da sakamakon kalubalantar zaben da jam’iyar Freedom ta shigar wanda dan takararta Norbert Hofer ya fadi zabe da karamar rata.
An kashe a kalla mutane shida lokacin da wani dan bindiga ya bude wuta kan wadansu motocin safa biyu a Kenya kusa da kan iyakar Somalia yau Juma’a.
Fitowar Najeriya a jerin kasashe marasa tabbas a duniya da asusun zaman lafiya dake birnin Washington DC ya bayyana a rahotansa na nuna yadda sunan Najeriyar ke daukar hankalin cibiyoyin bincike dana tattalin arziki da lamurrran labaru musammman ma ta fuskar tsaro.
Kasashen Isra’ila da Turkiyya sun cimma wata yarjejeniyar daidaita alakar da ke tsakanin kasashen biyu. Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ne ya bayyana haka a jiya Lahadi.
Firamistan rikon kwaryar kasar Spain Mariano Rajoy yace, tunda har jam’iyyarsa ta People’s Party ta cinye mafi yawancin kuri’un da aka maimaita kadasu a zaben ‘yan majalisa na jiya Lahadi, to kuwa ta sami damar ci gaba da shugabanci.
Matsalar Birtaniya ta kara zafafa a yau Litinin a daidai wannan lokacin da shugabannin Birtaniyar dana tarayyar Turai suke ta kokarin ganin sun shawo kan lamarin mai ban tsoro.
A karo na biyu gwamnatin tarayyar Najeriya ta kebe Naira Biliyan 90, domin raba lamani ga gwamnatocin jihohin kasar 36 su sami sukunin aiwatar da kasafinsu na bana, rahotanni na cewa 7 daga cikin jihohin ne kawai suka cika sharrudan sabon lamanin makonnin biyu bayan gwamnatin ta amince a bada kudaden.
Babbar kotun tarayya karkashin Alkali Yusufu Halluru, ta tura shugaban majalisar Dattawa Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu da tsohon jami’in gudanarwa na majalisar Salisu Mai Kasuwa da kuma wani mutum ‘daya zaman wakafi a gidan Yari.
Domin Kari