Wata cibiyar bincike mai zaman kanta a Ingila da ake kira IHS tace kungiyar ISIS tana kara hasarar yankunan da ada suke karkashinta a Iraqi da kuma Syria, kamar yadda cibiyar tayi bayani jiya lahadi.
Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yana kira ga shugabannin Sudan ta kudu, kasar da yaki ya daidaita, su takawa magoya bayansu wadanda suke dauke da makamai birki.
A Cambodia an harbe aka kashe wani dan gwagwarmayar siyasa kuma mai sharhi a kasar Kem Ley, da rana ido na ganin ido yayin da yake shan shayi a wani gidan mai Phnom Penh, a babban birnin kasar.
Tun bayan da wasu jami'an 'Yan sanda biyu farar fata suka harbe suka kashe bakar fata biyu makon jiya, ana ta zanga zanga a wurare daban daban a fadin kasar.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi watsi da rahotannin dake nuna cewa tsagerun Niger Delta na Bakassi Strike Force ne ke rike da ikon wasu kananan hukumomi biyu a jihar Cross River.
Majalisar yaran Najeriya mai suna Children Government Nigeria, ta baiwa gwamnatin tarayya kwanaki 30 da ta samar da abinci da kayayyakin more rayuwa ga yara da ‘yan gudun hijira dake sansanoni daban daban a fadin kasar.
Dagewar da ‘yan kungiyar matan neman ‘yan matan Chibok daga hannun ‘yan Boko Haram ta BBOG sukayai, na cewar ba zasu daina taro a Unity Fountain ba har sai an kwato dukkan ‘yan matan, na fusata wasu da suke ganin kungiyar na wuce gona da iri.
A cewar jami’an ma’aikatar tsaron Amurka, mutumin da aka kashe wanda ya kai hari kan jami’an ‘yan sanda a birnin Dallas dake jihar Texas, tsohon soja ne kuma yayi yaki a Afghanistan a baya.
Jami’an aikin jinkai sun yi gargadi yau Jumma’a cewa, karancin abinci ya yi Kamari ainun a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya da yaki ya daidaita, kuma yankin yana iya fuskantar matsalar karancin abinci.
A kokarin da gwamnati keyi na gano wanda ya kashe dan Majalisar Dokokin jihar Oyo, mai wakiltar mazabar Orelope, Gideon Aremu.
An bayyana wata ganawa da shugaban Amurka Barack Obama zai yi yau da abokan kawancen kungiyar tsaro ta NATO a matsayin taron kungiyar tsaron hadin guiwa mafi muhimmanci tun bayan karshen yakin cacar baki.
Amurka da Koriya ta Kudu sun sanar da shirinsu na tura na’urar kare makamai masu linzami zuwa kuryar Koriya domin dakile ayyukan nukiliya da makamai masu linzami da Koriya ta arewa take yi.
A wani yunkuri na ganin an samu dawwamamman zaman lafiya a jihar Adamawa, manyan sarakunan jihar sun gana da gwamnan jihar inda suka tabo hanyoyin samun zaman lafiya.
Shugaban Uganda, Yuweri Museveni ya ce kasar za ta sake yin dubi kan batun shirinta na janye dakarunta daga Somalia, idan har shirin wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika na AU ya daidaita.
Hare haren kunar bakin waken da aka kai a Saudiyya ya shafi manyan biranen kasar a jiya Litinin, ciki har da wanda aka kai a kusa da masallacin Manzon Allah tsira da amince su tabbata a gareshi, wanda ya halaka mutane hudu ya kuma raunata wasu mutane biyar.
Majalisar Dokokin jihar Niger tayi Allah wadai da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na biyan rabin albashin ma’aikatan gwamnatin jihar a dai dai wannan lokaci.
Hukumar wanzar da tsaro a jihar Plateau tace ta dauki tsauraran matakan tsaro a jihar don tabbatar da an gudanar da bukukuwan sallah lafiya.
Mazauna yankin Koh mai kunshe da kauyuka goma sha uku karkashin lemar kungiyarsu Njiya Ngoron na karamar hukumar Gerei, sun gabatar da kukan su gaban hukumar kare yancin ‘dan Adam ta Majilisar Dinkin Duniya suna bukatar gwamnatin jihar Adamawa ta biya diyyar naira biliyan biyu.
Domin Kari