A Libya, gwamnatin kasar ta 'hada kan kasa,' wacce Majalisar Dinkin Duniya ta shiga tsakani aka kafa, ta kira jakadan Faransa, bayan da aka goce da zanga zanga a Tripoli da ma a wasu sassan kasar, domin nuna adawa da kasancewar sojojin Faransa na musamman a kasar.