Tun bayan da kungiyar ta Human Rights Watch, ta fitar da rahoton dake bayyana yadda ake cin zarafin mata ta yin lalata dasu ta hanyar fin karfi da kuma yau dara a wasu sansanonin 'yan gudun hijira dake Arewa maso Gabashin Najeriya, yasa hankulan kungiyoyi kare hakkin bani adama ya shi, yayin da gwamnatin kasar ke cewa za’a yi bincike.