A hukumance an bayyana cewa mutane 26 ne suka rasa rayukansu a wani hari da wasu ‘yan bindiga suka kai a wata mahakar Zinari a kauyen Bindin na karamar hukumar Mulki Tamaru dake jihar Zamfara.
A yayin da Amurkawa ke fitowa kwansu da kwarkwatarsu domin kada kuri’un zaben sabo ko sabuwar shugaban kasa, mai cike da dinbin tarihi.
Biyo bayan takaddamar da ake a Philippines na cewa ko za a iya binne tsohon shugaban kasar Ferdinand Marcos, kan cewa ko za a iya binne shi a makabartar zaratan kasar.
An gano wani rami cike da gawarwakin wasu mutane da ake tsammanin anyi musu kisan gilla a kusa da birnin Mosul.
Dakarun Siriya da kurdawa ke jagoranta, tare da goyon bayan hare-hare ta sama da Amurka ta kai da kuma shawarwarin soja, sun taimaka wajen kwato wasu wuraren ‘yan ISIS a cikin gwabza wani kazamin fada jiya Litinin a Arewacin birnin Raqqa.
Yau Talata ne Amurkawa ke zuwa rumfunan zabe a fadin kasar don zaben sabon ko sabuwar shugaban kasa.
Kamar yadda hankalin Amurkawa ya karkata ga zaben shugaban kasa da gudanarwa a yau Talata, bisa ga dukkan alamu sauran al’ummar duniya sun saka ido domin gann yadda zata kaya.
Yayin da ake shirye shiryen gudanar da babban zaben shugaban kasa a Amurka, biyo bayan yawan kamfen da ‘yan tarar shugabancin kasar ke yi na ganin sun sami nasara a zaben da za a yi gobe Talata.
Baki daya ‘yan takarar shugabancin Amurka Hillary Clinton ta jam’iyyar Democrat da Donald Trump na jam’iyyar Republican sun mayar da hankalinsu akan wasu jihohi da suke bukatar ganin sun sami nasara a kansu.
A jamhuriyar Nijar ma’aikatan aikin hakar Man Fetur sun fara yajin aikin kwanaki biyu, domin nuna rashin jin dadin ga yadda shugabannin kamfanin CNPC ke fifita ma’aikata ‘yan kasar China fiye da su ‘yan kasa musamman kan batun shugabanci da albashi.
A baya dai anyi ta muhawarar cewa wasu sojojin dake filin daga a shiyyar Arewa maso Gabas na kwarmata bayanan sirri ga mayakan Boko Haram da hakan ke kawo tarnaki ga yaki da Boko Haram.
Noma Tushen Arziki
'Yar takarar shugabancin Amurka Hilary Clinton da Donald Trump duk sun gudanar da gangamin yakin neman zabe jiya Alhamis da dare a jahar Carolina ta Arewa-jahar da kusan tilas duk mai tsammanin zama shugaban Amurka tsakaninsu ya sami nasara zaben da za'a yi ranar Talata idan Allah Ya kaimu.
Darururwan 'Yan sandan Faransa ne suka fara rusa makeken sansanin bakin haure a Arewa maso Gabashin birnin Paris, a dai dai lokacin da gwamnati take kokarin kawar da duk bakin haure daga kan tituna zuwa wasu sansanoni ko wurare da gwamnati ta ware dmin haka. An dauki wannan matakin ne yau Jumma'a.
A Syria,wata yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa'o'i 10 da Rasha ta ayyana a birnin Aleppo, da yake-tsaka-mai-wuya, ta fara aiki.
Gwamnatin Najeriya na samarwa da rundunar sojojin ruwan kasar manyan jiragen yaki na zamani.
Kwamitin samar da zaman lafiya a yankin Agadez na kasar Jamhuriyar Nijar, ya dauki matakan gaggawa domin daukaka sha’anin tsaro a yankin dake fama da tashin hankali.
Duk kokarin da ma’aikatar tsaron Najeriya ke yi na samar da zaman lafiya a wasu garuruwan jihohin Ogun da Lagos, har yanzu ana kai wasu ‘yan hare hare.
A ci gaba da bikin cika shekaru goma da Sarkin Musulmi mai martaba Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III yayi kan karagar mulki a Sokoto.
A karon farko wata kotun tarayya dake jihar Lagos ta zartar da hukunci mai nasaba da cin hanci da rashawa da ya shafi uwargidan tsohon shugaban Najeriya, Madam Patience Jonathan.
Domin Kari