A Najeriya daukar ‘dalibai zuwa karatu a jami’o’in kasashen waje ya zama ruwan dare ga masu kudi da shugabannin siyasa, sai dai wasu na ganin zai fi muhimmanci a inganta jami’o’in dake cikin gida.
A jamhuriayr Nijar hukumomin kiwon lafiya sun kaddamar da shirin gwajin jini da baiwa jama’a magungunan kwantar da cutar sukari kyauta, albarkacin ranar da yaki da cutar sukari da ake kira Diabetes a turance, wanda ake bukin karramawa a yau 14 ga watan Nuwamba a ko ina cikin duniya.
A kalla mutane 9 ne suka rasa rayukansu wasu dayawa suka raunata a wata arangama da akayi tsakanin ‘yan kungiyar Shi’a da jami’an ‘yan sandan jihar Kano.
Noma Tushen Arziki
Yau Juma’a gwamnatin kasar Turkiyya ta tsare babban jami’in gudanarwar jaridar Cumhuriyat, bayan da ta tsare wasu ma’aikatan ta su 9 a cikin makon da ya gabata, kamar yadda jaridar ke cewa.
Wani alkali a nan Amurka ya shawarci zababben shugaban kasa da ya tabbatar ya kammala shara’ar almundahanar dake gaban sa na game jami’ar sa.
Dubun dubatan mutane a birnin New York dake gabashin Amurka, zuwa jihar California a dake Yamma sun cika manya-manyan tituna, yau suka shiga rana ta uku ta nuna kyamar su ga zaben Donald Trump a matsayin shugaban Amurka na 45.
Jami’an hukumar kula da shige da fice ta kasar Nijar tare da hadin gwiwar ‘yan sanda sun cafke duro duro da jarkokin Man Fetur, wadanda ‘yan fasa kwauri suka boye a wani kauye a birnin Yamai.
An gudanar da taron kasa na yini biyu kan bitar tafiyar da dimokaradiyya cikin shekaru 17 babu katsewa a Najeriya.
Shugaban Amurka Barack Obama ya gana da sabon zababben shugaba Donald Trump a fadar White House.
Dubban jama’a dauke da kwalayen dake yin tur da zababben shugaban Amurka Donald Trump sun yi zanga zanga.
Wasu ‘yan kungiyar Shi’a sun gudanar da zanga zangar neman a sako jagoransu Ibrahim El-Zakzaky, inda suka mamaye hukumar kare hakkin bil Adama ta Najeriya.
Yayin da ake cigaba da bayyana ra’ayi game da sakamakon zaben kasar Amurka, kungiyoyin mata a Najeriya ciki har da lauyoyi sun maida martani da cewa akwai abin dubawa ga makomar siyasar mata.
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya shiga jerin kasashen duniya da ke yiwa sabon zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump Murna.
Donald Trump shine ya zama zababben shugaban kasar Amurka.
A jiya Talata ne a ka kama wasu mutane guda biyar a kasar Jamus inda ake zarginsu da daukan mayakan kungiyar yan ta’adda ta Dae’sh. Ministan shari’a Heiko Mass ya kira kamen da “Sare gwiwa ga harkokin masu tsatstsauran ra’ayi a Jamus”.
Shugabar kasar Koriya ta Kudu, Park geun-hye, tace zata bar yan majalisar kasar su zabi sabon Firaminista , saboda tana kokarin tsallake rikice rikicen siyasar cikin gida da take fuskanta.
Biyo bayan jawabin da sabon zababben shugaban Amurka Donald Trump yayiwa magoya bayansa a hedikwatar gangamin yakin neman zabensa da ke birnin New York.
Zaben kasar Amurka da kuma sakamakon zaben da ya biyo baya, wani al’amarine da ya dauki hankalin duniya baki daya.
Mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo, ya kaddamar da shirin manufar kasa kan ruwa a wani taro da ya hada da gwamnoni da Kwamishinonin ruwa na kasar.
Domin Kari