Kungiyar direbobin Tirelolin masu dakon shanu daga kasuwar shanu ta kasa da kasa na garin Mubi, dake jihar Adamawa sun yi barazanar shiga yajin aiki saboda abin da suka kira tsangwama da cin mutunci da gallazawa na jami’ian tsaro akan hanyoyi don karbar na goro.
Ofishin jakadancin Amurka dake Abuja ya fitar da sanarwa inda ya nuna rashin jin dadi dangane da yadda aka kashe yan Shi’a a jihar Kano.
An sami tashin bama bamai a wasu wurare dabam dabam har guda uku a cikin garin Maiduguri, wanda yayi sanadiyar mutane shida wadanda akace guda hudu daga ciki dukkanninsu wadanda ke dauke da bama baman ne, guda biyun kuma ‘yan kungiyar Civilian JTF ne.
Kotun tsarin mulkin jamhuriyar Nijar ta sanar cewa ba ta da hurumin yanke hukunci akan wata karar da ‘yan adawa suka shigar a game da halaccin gwamnatin kasar.
A ganawar da Shugaba Mohammadu Buhari yayi da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry, ya tabbatar da cewa rashawa da cin hanci ya dawo yana yakar masu yaki da cin hanci da rashawar a Najeriya.
An shiga rana ta biyu da fara yajin aikin gargadi na tsawon mako guda da kungiyar malaman Jami’o’i ta Najeriya ta fara, a wani mataki na matsa lamba ga gwamnatin kasar ta mutunta yarjejeniyar da bangarorin biyu suka sanya a shekarun da suka gabata.
Shugaban Amurka Barack Obama ya jaddada muhimmancin mika mulki "cikin ruwan sanyi" a Amurka, yayinda yake jawabi ga al'umar kasaar Girka yau Laraba kan tsarin demokuradiyya.
Wani kwamitin Majalisar dinkin duniya jiya Talata ya amince da wani daftari da a ciki aka yi Allah wadai da mamayar da Rasha ta yiwa yankin Crimea, kudurin ya sake nanata cewa bai amince da kamawa da hade yankin na Crimea da Rasha da Moscow tayi.
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya gana da shugaban Najeriya Mohammadu Buhari, a gefen taron da ake na kasa da kasa kan dumamar yanayi a birnin Marrakech na kasar Morocco.
Majalisar Dattawan Najeriya tace zata shiga tsakanin kungiyar malaman Jami’o’i da bangaren gwamnatin tarayya, kan batun yajin aikin da kungiyar ke shirin tafiya.
Kimanin mutane Miliyan 14 ne zasu bukaci agajin gaggawa a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, kuma dubban yara zasu fuskanci matukar yunwa a yankin, a cewar jami’in jin ‘kai na Majalisar Dinkin Duniya mai kula da lamuran Najeriya Peter Lundberg.
Shugaba Mohammadu Buhari yayi jawabi a taron kasa da kasa da ake gudanarwa a kasar Morocco domin yin nazari da tsara hayar da za a yaki matsalar dumamar yanayi a Duniya.
Dubban jama’a ne suka halarci sallar jana’izar marigayi sarkin musulmi na 18 Alhaji Ibrahim Dazuki, a babban masallacin Juma’a na sarkin musulmi Bello dake Sokoto, karkashin jagorancin mai girma sarkin musulmi Mohammad Sa’ad Abubakar da mai girma sarkin Kano Mohammad Sunusi na biyu.
Gwamnatin kasar Saliyo ta kare karin farashin albarkatun man fetur da tayi a kasar. Gwamnatin kasar ta sanar a makon da ya gabata cewa zata cire tallafin man fetur, da kalanzir, da man diesel.
Shugaban Amurka mai barin gado Barack Obama yana Girka yau Talata, ya kuma kaiwa kasashen Turai tabbacin da suka dade suna jira akan kudurin Amurka ga rundunar NATO karkashin gwamnatin Donald Trump.
Rasha ta fada yau Talata cewa, sojojin saman ta sun kaddamar da wani babban farmaki a lardunan Idlib da Hom dake Siriya.
Gamayyar kungiyoyin yaki da cin hanci da rashawa daga jihohi 36 na Najeriya ne suka fara wani gagami na musamman a kofar Majalisar Dokokin Najeriya.
Amurka zata sayarwa Najeriya wasu jiragen yaki na zamani guda Goma sha Biyu don kawo karshen kungiyar Boko Haram.
Rundunar hadin gwiwa na ta kasashen yankin tafkin Chadi ta ce daruruwan mayakan Boko Haram ne suka mika wuya, yayin da ake ci gaba da samun karuwar hare haren a bangaren Najeriya.
A Najeriya kwararrun Injiniyoyin hanya sun baiyana goyon bayansu ga gwamnatin da ta kafa shingayen biyan kudi a manyan hanyoyin motar kasar da za'a gyara da zummar biyan kudin da za'ayi anfani dasu wajen kulawa da hanyoyin mota a Najeriya.
Domin Kari