Gwamnatin Amurka ta kashe kudi kimanin Dala Biliyan 3.4 domin yaki da cutar HIV mai karya garkuwar jiki a Najeriya.
Ba tare da yin amfani da kalmomin murabus ko tumbukewa ba, shugabar Koriya ta kudu Park Geun-hye ta bayyana niyyar sauka daga mukaminta a cikin lumana, muddin majalissar dokokin kasar ta bukaci tayi hakan.
Shugaban kasar Amurka mai jiran gado Donald Trump ya zabi dan majalissar wakilai daga jihar Georgia Tom Price, Wanda ya caccaki shirin kula da lafiya da shugaba Obama yayi, a matsayin wanda zai shugabanci ma’aikatar kiwon lafiya da kula da ayyukan jama’a.
Kasar Faransa ta kira taron gaggawa na Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya akan birnin Aleppo.
Gwamnatin Najeriya ta kara fayyace shirin ta na amfani da bangaren sufurin jirgin sama da jirgin ‘kasa wajen farfado da tattalin arzikin kasar.
Majalisar Dokokin jahar Lagos ta amince da dokar hukuncin kisa akan masu sata da garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a jahar.
Shugaban kasar Senegal Macky Sall ya kai ziyarar aiki kasar jamhuriyar Kamaru, domin yiwa takwaransa Paul Biya ta’aziyar hatsarin jirgin kasa da kuma karfafawa shugaban gwiwa a yakin da ake da Boko Haram.
Uku daga cikin Ministocin gwamnatin Shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu sun yi kira ga shugaban da yayi Murabus sakamakon abubuwan fallasa dake ta wakana game da shi.
Ana sa ran dubun dubatan mutane zasu yi cincirindo a shahararren filin nan na Revolutionary Square, ko dandalin Juyin Juya Hali na birnin Havana a yau litinin, yayin da kasar Cuba ta fara zaman makokin sati daya na yin ban kwana da marigayi Fidel Castro, mutumin da wasu ke matukar kauna, wasu kuma suke yin gaba da shi.
A ci gaba da gurfanar da manyan alkalan Najeriya gaban kotu bisa zarginsu da laifin cin hanci da rashawa, hukumar EFCC ta gurfanar da wata babbar Alkaliyar kotun tarayya.
Gwamnatin jahar Borno zata kafa sabuwar tashar jirgin ruwa a garin Maiduguri, don rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta.
Biyo bayan ayyana Oluwarotimi Odunayo Akeredolu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jahar Ondo, wasu mazauna jihar sun bayyana ra’ayoyinsu game da zaben.
Noma Tushen Arziki
Kimanin garuruwa 869 ne suka fuskanci fari cikin garuruwa 3,378 a jahar Damagaram, abin da yasa gwamnati daukan matakin shirin inganta noman rani, hakan ya biyo bayan wani rangadin da karamin Minista na ma'aikatar noma da kiwo yayi a jahar Damagaram.
An shiga kwana na hudu ana tashin hankali a birnin Bamenda na kasar jamhuriyar Kamaru, biyo bayan zanga zangar da kungiyoyin lauyoyi da na malaman makaranta.
An sami fashewar wani bom da missalin karfe tara na dare a kusa da wani gareji da ake kira Muna Garage dake garin Maiduguri, bam din ya kashe dan kunar bakin waken da kuma wasu mutane biyu.
Daruruwan ‘yan jam’iyyar PDP mata da maza sun gudanar da zanga zanga a birnin Akure don nuna jin dadinsu na musanya sunan Jimoh Ibrahim da Eyitayo Jegede a matsayin wanda zai yiwa jam’iyyar PDP takarar gwamna a jihar Ondo, biyo bayan hukuncin kotun daukaka kara.
Domin Kari