Gwamnonin arewacin Najeriya sun nemi takwarorinsu na kudu maso gabashin Najeriya da su ja kunnen matasan yankunansu da ke kalamai masu haifar da rarrabuwar kawuna a Najeriya, musamman ma shugaban kungiyar IPOB Nnamdi Kanu.
Majalisar dattawan Najeriya ta yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara, kadan daga cikin abubuwan da aka yi wa kwaskwarima, akwai dokar da ta ba matasa damar tsayawa takara a matakai daban-daban ciki har da na mukamin shugaban kasa.
Hukumar zabe ta INEC a Najeriya ta dora alhakin dakatar da shirin kiranye da take kokarin gudanarwa a kan Sanata Dino Melaye da ke wakiltar mazabar Kogi ta yamma a kan kotu.
Kungiyar Kiristoci ‘yan siyasa daga Shiyar Arewa sun yi kira ga gwamnatin Tarrayya da kakkausar Murya da ta dauki kwakwkwaran mataki akan shuwagabanin addini masu yin kalamai da ka iya tunzura al'uma.
Kungiyar fafutukar ganin an kwato ‘yan matan Chibok sun yi tattaki zuwa Aso Rock fadar shugaban kasa inda suka kai wani sabon sako.
Majalisar Wakilan Najeriya ta gayyaci shugaban hukumar Kwastan Kanar Hamid Ali mai ritaya, domin yayi mata bayanin dalilan da suka sa aka fara amfani da dokar hana shigowa da motoci ta iyakokin Najeriya bayan Majalisar ta ce a dakatar.