Rikita rikitar canjin takardun kudin naira ta dau wani sabon salo, bayan da kungiyar gwamnonin jihohin Najeriya ta bukaci a tsawaita wa'adin daina amfani da tsoffin takardun kudin zuwa shekara guda daga yanzu
Hukumar Alhazai ta kasa a Najeriya NAHCON ta kafa Cibiyar Kula da Aikin Hajji a domin horar da ma'aikatan da ke aikin Hajji da Umrah, wadda dalibai ma na iya karatu don samun shaidar babban digiri a cibiyar.
Kungiyar dillalan man fetur ta kasa zata fara samun ma kai tsaye daga kamfanin NNPC ba sai sun saya a hannun 'yan kasuwa ba. Kamfanin NNPC ya dauki wannan matakin ne domin saukaka karancin man da ake fama da shi a Najeriya, amma masu ruwa da tsaki na cewa ba girin-girin ba ta yi mai.
Kwararru a fanin gudanar da mulki da masu ruwa da tsaki sun baiyana ra'ayoyi mabanbanta akan hukuncin da Kotun Koli ta yanke, inda ta baiwa Sanata Ahmed Lawan daman tsayawa takara a kujeran Majalisar Dattawa a karkashin tutar Jamiyyar APC a jihar Yobe ta Arewa.
Hukumar zabe a babban birnin tarayyar Najeriya ta ce ta kintsa tsaf don gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan Majalisu, duk da yake birnin ba jiha ba ne, kuma ba shi da gwamna.
Wani kwamitin majalisar wakilan Najeriya ya ce majalisa ba ta amince da karin wa'adin da babban bankin Najeriya yi ba, kuma majalisa na iya shigar da kara kotu domin ta ga cewa an tsawaita wa'adin canjin kudin fiye da wata shida idan bukatar haka ta kama.
Rahoton da babban bankin Najeriya ya fitar a shafinsa na yanar gizo ya ce bankin ya kashe dalar Amurka biliyan 11.42 a cikin watanni 7, daga watan Janairu zuwa watan Yuli na shekarar 2022 domin a farfado da darajar naira.
A yayin da ya rage kwanaki bakwai a kammalla sauya tsofaffin takardun kudi na Naira 1000, Naira 500 da Naira 200, manyan 'yan siyasa da masu ruwa da tsaki sun koka cewa har yanzu akwai karancin sabbin kudi a bankunan kasuwanci musamman a Abuja.
Kwamitin Majalisar Dattawa mai Kula da harkokin 'yan sanda ya saurari bahasin Jama'a akan wani kudurin doka da zai bada dama a kafa hukumar kula da fansho na 'yansanda.
Jamiyyar APC mai mulki ta yi kira ga hukumar EFCC da ICPC da su kama dan takaran kujeran shugaban kasa na jamiyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar akan zargin da aka yi cewa an hada baki da shi an yi sama da fadi da dukiyar al'umman Najeriya.
Sa'o'i kadan bayan da kamfanin NNPC ya bada sanarwar samun Man fetur a Jihar Nasarawa da ke Arewa ta tsakiya a Najeriya, masu ruwa da tsaki sun bada ra'ayoyi mabanbanta a game da al'amarin.
Kwamitin Kula da Harkokin Makamashi a Majalisar Wakilan Najeriya ya yi taron sauraren ba'asin jama'a kan yunkurin gyara dokar samar da wutar lantarki ta shekara 2005, don samar da tsarin doka da daidaita aiwatar da ayyukan samar da wutar lantarki.
A wata sanarwa da darekta janar na ofishin sayar da kaddarorin gwamnati wato BPE Alex Okoh ya fitar, ya nuna cewa za a sayar da kamfanonin wuta biyar a kwatan farko na wannan shekara da muka shiga, domin samar da kudade da za a cike gibin Kasafin kudin shekara 2023 da su.
A cigaba da takaddamar da ake yi kan batun sauya fasalin naira, Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya tsawaita wa'adin canja kudade a Najeriya.
Ga dukkan alamu har yanzu da sauran rina a kaba game da takaddamar bangaren Majalisar Dattawan Najeriya da bangaren zartaswa kan maganar kudin da aka kashe, ko za a kashe. Hasali ma, wannan gardama ce kan halaccin kudin da aka kashe.
Bankin Duniya ( World Bank) ya sake sukar salon tsarin canjin Kudi na Babban Bankin Najeriya a daidai lokacin da ra'ayoyi tsakanin masana tattalin arziki da manazarta suka banbanta akan yadda ake sayar da dala daya wanda a yanzu ya kama Naira 760 a kasuwar bayan fage a maimakon Naira 445.
Sake fasalin naira da Babban Bankin Najeriya ya yi ya ja hankalin Bankin Duniya wato World Bank.
Mataimakiyar Gwamna a Babban Bankin Najeriya CBN, Aisha Ahmed ta ce sun yi odar sabbin kudin da aka sauya fasalinsu har na Naira miliyan dari biyar, amma ta gagara fadin ko nawa aka kashe wajen buga su.
Majalisar Dokokin Najeriya ta daga zartar da kasafin kudin shekarar 2023 da ya kamata ta yi a jiya alhamis zuwa mako mai zuwa saboda matsalolin da aka gano a cikin kasafin
A karo na biyu jiya Talata gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya sake kin amsa gaiyatar Majalisar wakilai a bisa hujjar cewa bai dawo daga kasar waje ba.
Domin Kari