Shugaban Amurka Joe Biden, ya zabi ba’amurkiya ‘yar asalin Najeriya a matsayin mukaddashiyar shugabar hukumar bunkasa harkokin kasuwancin kasar ta USTDA.
Aikin tiyatar da aka yi wa fitaccen dan wasan golf din Amurka Tiger Woods ya yi nasara kuma yana samun sauki, a cewar wata sanarwa da aka wallafa a shafinsa na Twitter.
Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da rufe daukacin makarantun kwana da ke jihar biyo bayan sace dalibai sama da 300 da aka yi.
Ana ci gaba duba yiwuwar farfado da matsayar da aka cimma kan shirin nukiliyan Iran, tsakanin hukumomin Tehran da sauran kasashe da ke cikin wannan yarjejeniya, yayin da Amurka da Iran suka nuna sha'awar hakan.
Fitaccen mawakin kasar Canada Justin Bieber, ya fara bin matashin mawakin Najeriya Omah Lay a dandalin sada zumunta na Instagram.
Cikin yanayi mai cike da alhini, an gudanar da jana’izar dakarun saman Najeriya nan bakwai da suka gamu da ajalinsu a hatsarin jirign sama.
Shahararren mawakin Amurka Stevie Wonder ya ce zai koma kasar Ghana da zama yana mai nuni da yadda rikicin siyasar Amurka ya tabarbare.
Fitacce dan wasan kwallon golf din Amurka Tiger Woods ya yi wani mummunan hatsari a cewar ofishin ‘yan sandan birnin Los Angeles.
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya kyankyasa inda yake ganin masu garkuwa da mutane suka boye daliban makarantar Kwalejin Kimiyya ta Kagara da ke jihar Neja.
Yayin da jama'ar Jamhuriyar Nijar ke dakon sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi a ranar Lahadi, bayanai na nuni da cewa, tsohon ministan cikin gida Bazoum Mohamed ne ke gaba a kidayar kuri'un da ake yi.
Cristiano Ronaldo ya kara haurawa da Juventus saman teburin cin kofin gasar 'Seria A' ta Italiya bayan da ya zuba kwallaye biyu duka da ka a karawarsu da Crotone.
Rundunar sojin saman Najeriya na ci gaba da yin karin haske dangane da hatsarin da jirgin samanta ya yi wanda ya halaka mutum bakwai.
Ma’aurata kuma fitattun jarumai a masana'antar shirya fina-finai ta Nollywood da ke Najeriya, Olubankole Wellington, wanda aka fi sani da Banky W da matarsa Adesua Atomi- Wellington, sun haihu.
Kasuwar hannayen jarin Najeriya ta ci gaba da fuskantar tawaya bayan da ta fadi da Naira biliyan 130 a makon da ya gabata.
Karawar hamayya ta cikin gida da aka yi ta ba Inter Milan damar wanke AC Milan da ci 3-0 lamarin da ya sa ta samu nasarar kara fadada tazarar da ke tsakaninsu.
Jamhuriyar Nijar ta dauki hanyar kafa tarihi, inda a karon farko zababbiyar gwammatin farar hula za ta mika mulki ga wata takwararta ta farar hula ba tare da wata tangarda ba.
Hukumomi a wani yanki da ke wajen birnin New Orleans a jihar Louisiana sun ce wani mutum ya shiga wani shagon da ake sayar da bindiga ya kashe mutum biyu.
Bayan da ta buga wasa 68 ba tare da an kada ita ba, Liverppol ta sha kaye a wasa hudu na baya-bayan nan da ta buga a gasar Premier League.
Al’umar Jamhuriyar Nijar ta fita rumfunan zabe don kada kuri’a a zaben shugaban kasa da ake yi zagaye na biyu.
Alkaluman da hukumomi suka fitar a karshen makon nan a Najeriya sun nuna cewa kasar ta fita daga tawayar tattalin arzikin da take fuskanta.
Domin Kari