A karo na 11 an samu wani Ba'amurke da ke dauke da cutar Ebola bayan da ya je aikin jin kai a kasar Saliyo.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya yi ikrarin cewa kungiyar Boko Haram na samun horo daga kungiyoyin Islama da ke Gabas ta Tsakiya. Shugaban ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da VOA.
Wani tasiri da hukuncin daurin shekaru 20 da wata kotu ta yi wa tsohuwar matar shugaban Ivory Coast shi ne zai zama darasi ga sauran shugabannin, sai dai a wani bangaren masu sharhi na cewa hukuncin ya farfado da kiyayyar da ke tsakanin magoya bayan Laurent Gbagbo da na shugaba Alassane Ouattara.
A Jamhuriyar Nijar an kaddamar da shirin kayata birnin Maradi a wani mataki na maida birnin zuwa cikakke birni na zamani.
Yayin da ake tunkarar zabe a ranar 28 ga wannan wata na Maris, rahotanni na cewa 'yan sanda a Najeriya na barazanar shiga yajin aiki.
A karshen makon da ya gabata ne Kungiyar Boko Haram da ke ta da kayar baya a Najeriya ta yi mubayi'a ga kungiyar ISIS mai da'awar kafa daula musulunci. Ko ya ya masana su ke kallon wannan mataki da kungiyar ta dauka?
Kokarin nemo bakin zaren rikicin kasar Sudan ta Kudu ya sake samun cikasa bayan da aka kammala taro a yau juma'a ba tare da an samu matsaya guda ba.
A kokarin da ta ke yi ta ga cewa ba a bar 'yan makarantar firaimare a baya ba, gwamnatin Kamaru ta kaddamar da wani shirin gina makarantu bayan da 'yan kungiyar Boko Haram su ka rusa wasu da dama.
Iyayen 'yan matan Chibok da a ka sace sun maida martani ga gwamnati inda su ka ce sun gaji da gafara sa kuma ko kaho ba sa gani.
Bayan kwato wasu garuruwa da dakarun hadin gwiwa hade da na Najeriya su ka yi, gwamnatin kasar ta ce ta dauki matakan kare aukuwar hakan.
Yayin da ake kokarin inganta matakan tsaro a Najeriya saboda zabe mai gabatowa sai ga shi wani harin bam ya halaka wani dan sanda tare da raunata wasu da dama a Jihar Rivers.
Duk da cewa akwai barazanar kai hare-hare yayin da Najeriya ke tunkarar zabe a wannan wata mata da dama sun kudari aniyar za su fita su kada kuri'unsu.
Yayin da zaben Najeriya ke ci gaba da karatowa ana kai ruwa rana game da yin amfani da na'urar tantance katin zabe.