Kungiyar Boko Haram da ta samo asali daga Najeriya ta kai wani hari a yankin a garin Koukwandou da ke jihar Diffa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar.
Sabon rikicin siyasar kasar Burundi ya kuma lakume ran mutum guda, yayin da masu zanga zanga da ke ci gaba da nuna adawa kan yunkurin da shugaba Pierre Nkurunziza ke yi na sake tsaya takara a zabe mai zuwa.
Akalla mutane 200 rahotanni daga Jamhuriyar Niger ke cewa sun mutu sakamakon cutar sankarau da ta addabi yankin Yamai, babban birnin kasar.
A watan Mayun shekarar 2012, gwamnatin Jihar Kano ta fito da wani tsarin aurar da daruruwan zaurawa a wani mataki na ganin an dakile matsalar yawan mace-macen aure a jihar.
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta sake kubutar da wasu mata daga dajin Sambisa kwanaki biyu bayan da ta ceto wasu ‘yan mata da manyan mata kusan 300.
Jiragen yakin Syria sun yi ruwan bama-bamai a Jisr al-Shughour dake arewa maso yammacin kasar a yau din nan lahadi. Kwana daya bayan kungiyar Nusra Front masu alaka da Al-Qaeda sun kwace garin a karo na farko a shekara hudu da ake yakin kasar.
Hukumar zabe a jihar Taraba, ta bayyana jam’iyyar PDP a matsayin wacce ta lashe zaben gwamna da aka gudanar a jiya asabar.
An yi girgizar kasa mai tsananin maki 7.8 a kasar Nepal wadda ta halaka mutane sama da 700.
Tsohon gwamnan jihar Filato, Ambasada Fidelis Tapgun, ya kwatanta masu ficewa daga PDP suna komawa jam’iyyar APC a matsayin ‘yan ci rani, ya na mai cewa hakan ba dai dai ba ne.
Shekaru 16 bayan kisan tsohon shugaban kasar Jamhuriyar Niger Ibrahim Ba’are Mai Nasara, kotun Kungiyar kasashen Yammacin Afrika ta ECOWAS ko kuma CEDEAO da ke Abuja, ta baiwa iyalan marigayin damar yin bayani a gabanta.
Kwanaki biyu bayan da kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wutar sojojin larabawa da Saudi ke jagoranta a Yemen, wasu jiragen yaki sun yi lugudan wuta a kan ‘yan tawayen shi’an Houthi.
A yau Alhamis Shugabannin kasashen Turai suna taro a Brussels domin shawo kan matsalar bakin haure daga nahiyar Afrika zuwa Turai, suna son daukar mataki ko da na karfin soji, bayan mutuwar mutane sama da 900 da jiragensu suka kife a cikin tekun Madetareniya.
Rahotanni daga jihar Taraba a arewa maso gabashin Najeriya, na cewa hukumar zaben jihar ta INEC ta ce ta shiryawa zaben raba gardama na gwamna da za a sake a jihar a ranar asabar mai zuwa.
A Najeriya, kotunan sauraren korafe-korafen zabe za su fara aiki, inda yanzu haka a Kano, jam'iyyar MPPP ke so soke zabukan da aka yi na 'yan majalisun tarayyan jihar.
Mutanen yankin arewa maso gabashin Najeriya sun fara nuna bukatar kafa wata hukuma da za ta taimaka wajen farfado da tattalin arzikin yankin.
A Najeriya rahotanni na cewa sabuwar gwamnati mai zuwa na shirin gudanar da bincike a kamfanin man fetur din kasar na NNPC tare da shirin tsaga shi zuwa bangare hudu.
Yayin da rage makwanni kadan jam'iya mai mulki ta PDP ta mika ragamar mulkin kasar ga zababbiyar gwamnatin APC, Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ce ya yanke shawarar mika mulki a ranar 28 ga watan Mayu maimakon ranar 29.
A Kudu Maso Kudancin Najeriya, rikici ya haddasa asarar rayukan mutane takwas a jihar Rivers yayin da jam'iyyar APC ta nemi a soke zaben jihar Akwa Ibom.
Mutane a ciki da wajen Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu game da abin da zababben shugaban kasar Najeriya janar Muhammadu Buhari ya kamata ya tunkura bayan lashe zaben da ya yi a karshen makon da ya gabata.
Rahotanni daga Najeriya na cewa Shugaba Goodluck Jonathan ya kira janar Muhammadu Buhari ya taya shi murna.
Domin Kari