Shugaban Amurka Donald Trump ya yi Allah wadai da karin sakonnin barazanar da ake aikawa al’umar Yahudawa a duk fadin kasar, wadanda ke nuna cewa ana kyamatar su.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake tsawaita hutun da ya tafi domin neman magani a London a karo na biyu.
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai kalubalanci hukuncin da wata kotun daukaka kara ta yanke, kan watsi da bukatar da ya gabatar mata na maido da umurnin nan da ya ya bayar na hana wasu ‘yan kasashe bakwai shiga Amurka.
Najeriya kasace da ta yi kaurin suna wajen zarge-zarge cin zarafin bil adama da jami'an tsaro ke yi idan aka la'akkari da rahotannin da kungiyoyi kare hakkokin bil adama da dama suka sha fitar a baya.
Wani Alkali a Rasha ya yankewa shugaban ‘yan adawa Alexei Navalny hukuncin je-ka-gyara-halinka na tsawon shekaru biyar, bayan da aka same shi da laifin yin almubazzaranci.
Majalisar Dattawan Amurka ta amince da zabin Rex Tillerson, tsohon shugaban kamfanin mai na Exxon Mobile a matsayin Sakataren Harkokin Wajen Amurka.
Jami’yun siyasa a Jamhuriyar Dimokradiyar Congo sun cimma wata matsaya a karshen makon da ya gabata, wacce ta nemi shugaba Joseph Kabila ya sauka daga mulki a karshen 2017.
Fitacciyar ‘yar wasan kwaikwayon Amurka, Carrie Fisher mai fitowa a fina-finan "Star Wars" ta rasu ta na mai shekaru 60.
Yayin da dakarun Najeriya ke ci gaba da ba da tabbacin cewa daukacin dajin Sambisa ya koma hanunsu, bayan da suka fatattaki mayakan Boko Haram a sansaninsu, masana na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan lamari.
Ma’aikatar tsaron Rasha ta ce wani jirgi dauke da sojojin kasar su 92, ciki har da shahararrun mawakan bege, ya fada a Tekun Bahrul Aswad, wato Black Sea, jim kadan bayan ya tashi a wajen wani shakatawa da ke garin Sochi
Kiristoci a Najeriya sun bi sahun sauran takwarosinsu na addini a duk fadin duniya wajen fara bukukuwan Kirsimeti.
Kungiyar ECOWAS ko kuma CEDEAO ta bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika, ta yi barazanar yin amfani da karfin tuwo wajen kawar da gwamnatin shugaba Yahya Jammeh na Gambia, muddin ya ki sauka daga kan mulki idan wa’adinsa ya kare a watan Gobe.
Firai ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya fara daukan matakan diplomasiyya akan kasashen da suka goyi bayan kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya nemi Isra’ilan ta dakatar da gine-gine da ta ke yi a yamma da kogin Jordan da kuma gabashin birnin Kudus.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce a yau Asabar, dakarun kasar sun karbe ikon wani sansanin kungiyar Boko Haram da ke cikin dajin Sambisa, wanda ya kasance tunga ga mayakan.
Rahotanni daga Najeriya na cewa 'yan matan Chibok 21 da aka kubutar a watan Oktoban da ya gabata sun isa birnin Yola domin komawa gidajensu su gudanar da bukuwan kirsimeti da za a fara a gobe a Lahadi.
Shugaban Amurka Mai Jiran-gado, Donald Trump, ya ce Amurka ba ta bukatar jirgin ruwanta mara matuki da China ta kama, saboda haka ta rike.
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadu Issuhu ya ce ba shi da niyyar yin tazarce a karshen wannan wa'adin da ya ke kai, kamar wasu bayanai ke yawo a kasar.
Yayin da kwamitin gwamnatin tarayya da aka kafa domin farfado da yankin arewa maso gabashin Najeriya ya isa jihar Adamawa, al’umar yankin sun ce babbar bukatarsu ita ce a maido da matakan tsaro
Shugaban Amurka Barack Obama ya ce, ya fito karara ya fadawa takwaran aikinsa na Rasha Vladmir Putin da ya dakatar da kutsen da Rashan ke yi akan Amurka, ko kuma Rashan za ta dandana kudarta.
Domin Kari