A yayin da daliban makarantun firamare da sakandare su ka koma makaranta jiya Litinin, kungiyar iyaye da malaman makaranta ta kasa wato P.T.A ta ce tun da har yanzu akwai matsalar tsaro, ya kamata gwamnati ta bada dama iyayen daliban su dauki mafarauta aikin kare makarantun Najeriya.
Kungiyar bincike da bunkasa Arewacin Najeriya ta ce hada kan al'ummar arewa ba tare da la'akari da bambancin yare, kabila ko addini ba, shi zai magance matsalolin da ke addabar yankin.
Kwanaki kadan da sakin Sadiq Ango Abdullahi, daya daga cikin 'ya'yan shugaban kungiyar dattawan Arewachin Najeriya, Farfesa Ango Abdullahi, wasu 'yan bindiga sun sake sace wasu dangin Farfesan a mahaifarsa ta Yakawada da ke karamar hukumar Giwa, Jihar Kaduna.
Bayan kwashe sama da kwanaki 135, 'yan-bindigan da su ka sace mutane a jirgin kasan Abuja-Kaduna sun sake sako wasu mutane bakwai a yau Laraba sakamakon shiga tsakani da daya daga cikin malaman addinin Musulunchi, Dr. Ahmad Mahmud Gumi ya yi.
Daya daga cikin fasinjojin jirgin kasar Kadauna-Abuja da mahara su ka saki a baya bayan nan ya bayyana yadda su ka yi rayuwa a hannun 'yan bindigar,
Bayan kwashe sama da watanni hudu a daji, 'yan-bindigan da su ka sace mutane a jirgin kasan Abuja-Kaduna sun kuma sake sakin wasu mutane biyar cikin fasinjojin da ke hannun su.
Sa'o'i kadan da sakin faya-fayan bidiyo har biyu na mutanen da 'yan-bindiga su ka sace a jirgin kasan Abuja-Kaduna, a Litinin din nan da rana, 'yan-bindigan sun sake sakin wasu mutane uku cikin wadanda aka nuna su na dukan su cikin faifan bidiyon jiya Lahadi.
Shugaban kamfanin jaridar Desert Herald da ya shiga tsakanin 'yan-bindiga da iyalan mutanen da aka sace a jirgin kasan Abuja-Kaduna, Malam Tukur Mamu da kuma 'yan-uwan wadanda aka sacen sun tabbatar da sahihancin faifan bidiyon da ke yawo a yanar gizo inda 'yan-bindiga ke dukan mutanen.
Al'umar karamar hukumar Birnin Gwari sun ce sabuwar kungiyar nan mai kama da ta Boko Haram da ake kira Ansaru na kara karfi a wasu sassan karamar hukumar kuma har shugabaanni ta sun hana mutanen yankin shiga harkokin zabe.
Duk da artabun da aka yi tsakanin 'yan-bindiga da wasu jami'an tsaron da su ka sami hadin kan 'yan- sintiri a kudancin karamar hukumar Birnin Gwari a jahar Kaduna, 'yan-bindigan su sake kai wani hari inda su ka kashe wasu manoma a yankin Ganin-Gari na karamar hukumar.
Muryar Amurka ta yi hira da daya daga cikin mutane bakwai da 'yan bindiga su ka saki na baya bayan nan, daga cikin fasinjojin jirgin kasar da aka yi garkuwa da su sama da kwanaki dari da su ka shige.
Bayanai sun yi nuni da cewa har yanzu akwai sauran mutum 44 a hannun 'yan bindigar dajin.
Domin Kari