Yanzu haka al’ummomin da suka koma yankunansu da aka kwato daga hannun mayakan Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya na kokawa game da batun rashin sabunta katunan zabensu.
A karshen makon jiya ne hukumar UNDP tare da hadin gwiwa da gwamnatin kasar Japan suka kaddamar da shirin bada kayan noma kyauta ga mazauna kauyen Loko, na karamar hukumar Song a jihar Adamawa.
A cikin ‘yan kwanakin nan rahotanni na nuna cewa mayakan kungiyar Boko Haram suna sauya salon kai hare-harensu ciki har da kisan dauki daidai, da kuma na sari-ka-noke, da kona kauyuka ko kuma dasa bama bamai a gonaki.
Wasu mahara sun kai wani sabon hari a garin Kacalla dake jihar Taraba inda aka samu asarar rayuka,ciki har da na mai garin
Magoya bayan gwamnan Jihar Gombe Ibrahim Dankwambo sun ce ba za ta sabu ba bindiga a ruwa, bayan da gwamnatin jihar Adamawa ta sa aka cire allunan kamfe dinsa na takarar shugaban kasa.
Wasu mahara sun sake kai wasu sabbin hare-hare a wasu rugayen Fulani na kananan hukumomin Demsa da Mayo Belwa a wani yanayi mai kama da fadan kabilanci.
Ana ci gaba da samun kwararar ‘yan gudun hijira biyo bayan wasu hare-haren da aka kaiwa wasu kauyukan Fulani a karamar hukumar Lau cikin jihar Taraba.
A dai dai lokacin da ake ci gaba da cece-kuce game da zabukan shugabanin jam’iyar APC a matakin jihohi da aka kammala a jiya asabar, yanzu haka hukumar zabe, INEC a jihar Adamawa tace bangare guda kawai ta sani, kuma da ita zata yi aiki.
Rahotanni dai sun bayyana cewa yanzu haka al’ummomin kauyukan Wadukun da Kwoh zuwa bangaren Tigno dake karamar hukumar Lamurde, cikin jihar Adamawan na cikin zaman dar-dar lamarin da yasa wasu mazauna yankunan kauracewa gidajensu.
Yayin da ake haramar fara azumin watan Ramadan a jihohin Adamawa da Taraba an tsaurara matakan tsaro don kare rayuka.
Hadakar kungiyar makiyayan Najeriya ta maida martani game da kisan da sojoji suka yiwa wasu Fulani makiyaya sama da goma a yankin Katibu, dake karamar hukumar Lau a jihar Taraba.
Yayin da alkaluman mutanen da suka mutu a tagwayen harin kunar bakin wake da aka kai garin Mubi ke karuwa, yanzu haka an garzaya da wadanda ke da munanan raunuka zuwa cibiyar lafiya dake fadar jihar wato FMC Yola.
A daidai lokacin da ake neman bakin zaren magance matsalolin tashe-tashen hankula da rikicin Boko Haram, yanzu cibiyar wanzar da zaman lafiya ta Amurka da ake kira ‘US Institute of Peace’ ta isa Najeriya tare alkawarin taimakawa don magance matsalar.
Direbobi sun rufe babbar hanyar da ta hada Adamawa da jihar Taraba sakamakon matsa musu da karbar na goro da jami'an tsaro ke yi.
A daidai lokacin da ake juyayin cika shekaru hudu da sace ‘yan matan Chibok da ‘yan Boko Haram suka yi a arewa maso gabashin Najeriya, yanzu haka iyayen daliban na barazanar zuwa kotun duniya.
Kiristoci a fadin duniya sun fara gudanar da bukukuwan Easter, domin tunawa da zagayowar ranar da aka gicce Yesu Almasihu, yayin da shugabannin addinai a Najeriya ke kira na musamman kan zaman lafiya da fahimtar juna.
Domin Kari