Batun tabarbarewar tsaro da kuma kuncin tattalin arziki su ka fi zama abubuwan tattaunawa a tsakanin ‘yan Najeriya musamman talakawa kan mulkin shugaba Buhari na shekaru 8.
Biyo bayan biris da gwamnatin Najeriya tayi na barazanar shiga yajin aiki da Kungiyar likitoci masu neman kwarewa NARD ta yi sati biyu da suka gabata, idan har gwamanti ba ta biya musu bukatunsu da hakkokinsu ba, kungiyar likitocin ta tsunduma yajin aikin gargadi na kwanaki biyar.
Shirin ya tattauna da masu kayan masarufi da kuma kayan sawa musamman a wannan lokaci da ake tunkarar karamarSallah.
Shugaban majalisar malamai na kungiyar Izala na Najeriya Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce ta hanyar raya ilimi ne kungoiyoyin addini za su ba da gudunmawa wajen yaki da talauci da miyagun dabi’u.
Shirin ya samu bakuncin Dr. Adama Ibrahim Jibril wanda ya yi karin haske kan abincin da ya kamata mutane su ci a lokacin bude-baki da sahur.
Masu sa ido kan lamuran yau da kullum a Najeriya na hasashen cewa kayan masarufi a bana zasu yi tsada saboda karancin kudi a hannun ‘yan kasar.
A duk lokacin aka buga gangar siyasa a Najeriya, gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu suke fara hada karfi da karfe wajen wayar da kan matasa da kuma yi musu gargadi da kada su bari ayi amfani da su wajen tayar da tarzoma a lokacin zabe, tare da yin nuni da irin illolin da ke tattare da hakan.
LAFIYA UWAR JIKI: Shafe-shafen Mayukan Sauya Kalar Fata “Bleaching” Da Illolinsu, Maris 16, 2023
A lokacin da ake gab da gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a Najeriya, karancin man fetur na ci gaba da ci wa ‘yan kasar tuwo a kwarya, da hakan zai iya zama matsala wajen yin tafiye-tafiye zuwa jihohi don gudanar da zaben.
A cikin shirin na wannan makon mun tattauna ne akan makanta ko rashin gani da wasu cututtuka ke haddasawa wanda kuma za'a iya kaucewa aukuwar hakan
A cikin shirin na wannan makon mun tattauna ne akan kaciya ko yankan gishiri da ake yi wa mata a wasu sassan da dama a fadin duniya, wanda a shekarun baya wannan abu ya yadu tsakanin mata da dama saboda wasu dalilai.
A duk rumfunan da Muryar Amurka ta ziyarta a Abuja an ga mata da yawa akan layi, ko dai sun kada kuri’arsu ko kuma suna jira su kada kuri’ar.
Tun farar safiyar yau Asabar da hukumar INEC ta tabbatar cewa za a gudanar da zaben shekarar 2023, a nan babban birnin tarayya Abuja mutane suka fito rumfunan zabe domin kada kuri’ar su.
Domin Kari