Rundunar sojojin saman Najeriya na bukin cika shekaru 54 da kafuwa, tare da duba ire-iren nasarorin da rundunar ta cimma cikin wadannan shekarun.
Kwamitin farfado da yankin arewa maso gabashin Najeriya, ya mayar da hankali wajen bunkasa kiwon lafiya musamman a matakin farko don inganta rayuwar al’ummar yankin.
A Najeriya an kawo karshen taron manyan hafsoshin sojojin Afirka da rundunar sojan Amurka ta shirya da zummar kawo karshen matsalar tsaro a nahiyar.
Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya PDP ta yi watsi da ayyana sake yin takara da shugaba Mohammadu Buhari yayi.
Hedikwatar rundunar sojojin Najeriya ta gudanar da wani taro kan samarwa dakarunta makamai don ci gaba da tunkarar matsalolin tsaro a kasar.
Kungiyar da ke rajin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya SERAP ta nemi gwamnatin tarayya ta janye jerin sunayen mutane shida da aka ce sune suka wawure dukiyar kasar.
Rahotanni daga Najeriya na cewa daliban makarantar Dapchi da kungiyar Boko Haram ta sace ta kuma sako su, sun koma gida bayan da aka kai su Abuja, babban birnin Najeriya.
Fadar shugaban kasar Najeriya ta tabbatarwa da Muryar Amurka cewa ‘yan kungiyar Boko Haram sun sako ‘yan matan Dapchi yau Laraba, amma kungiyar Amnesty International ta jaddada cewa dole sai an gudanar da bincike.
Shugaban ‘Yan sandan Najeriya ya ce a Janye daukacin ‘Yan sandan da ke tsaron wasu daga cikin fitattun mutane, domin a kara samar da cikakken tsaro a kasar.
Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, ya ce gwamnatin taryaya ta damu matuka da sace ‘yan matan Dapchi, sai dai masana na nuna damuwa kan rashin matakan tsaro tun kafin a sace ‘yan matan.
Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC tace ba za ta amince da yadda gwamnatoci jihohi ke ci gaba da takura ‘yancin kananan hukumomi ba, kasancewa suma hukumomi ne masu zaman kansu bisa kundin tsarin mulkin kasar.
Rundunar sojin saman Najeriya ta shirya taron bita na musamman ga ‘yan jaridar dake bada rahotannin tsaro a kasar, kan yadda zasu hada rahotannin tsaro tare da kaucewa haddasa fitina.
Shugabannin tsaron Najeriya zasu bayyana gaban Majalisar Dattawa domin yin bayani kan yadda aka sace 'yan matan Dapchi da kuma kokarin da suke na ganin an nemo 'yan matan.
A taron tsaro da kwalajin koyar da dabarun yaki ta rundunar sojojin Najeriya ta shirya, mataimakin shugaban Najeriya ya sake jaddada cewa sojoji sun karya lagon Boko Haram duk da cewa sai kara ta'azzara kungiyar ta keyi a jihohin Yobe, Borno da Adamawa
Sojojin dake atisayin tseren bera a wasu jihohin dake tsakiyar Najeriya sun kai dauki a karamar hukumar Numan cikin jihar Adamawa inda suka kashe makiyaya goma cikin wadanda suka kona garin Gomba kurmus
Taron kwanaki uku da Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Osinbajo ya bude a Abuja, na da zummar farfado da tafkin Chadi wanda cikin shekaru 20 da suka shude kashi casa'in na ruwansa suka bushe kana rikicin Boko Haram ya daidaita mutane fiye da miliyan tara a yankin.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayar da sanarwa cikin daren nan cewa ta kama manyan shugabannin da suka kitsa kai mummunan harin da ya hallaka mutane fiye da arba'in a Jihar Zamfara
A karon farko injiniyoyin sojojin saman Najeriya sun sami nasarar kera jirgin leken asiri maras matuki da aka sawa suna Tsegumi, wanda za a rika sarrafa shi daga kasa
Babban hafsa mai kula da sashen aikace-aikace da atusaye yace wannan rawar dajin za a yi a jihohin Binuwai da Taraba, za a kuma kara hadawa da jihohin Nassarawa, Kaduna, Neja da Kogi
Yayin da babban Sakataren hukumar inshorar lafiya ta Najeriya ya koma bakin, ana ci gaba da samun ra’ayi mabanbanta kan komawarsa aiki, bayan dakatar da shi da aka yi na tsawon watanni takwas, lamarin da ya janyo cece-ku-ce.
Domin Kari