Najeriya ta kasance daya daga cikin jerin kasashen da suka saba sayen kayayyaki irinsu mai, karafuna, takin zamani da dai sauransu daga kasashen ketare, to sai dai sakamakon yaki tsakanin Rasha da Ukraine, a halin yanzu masana sun yi hasashen cewa matsalar yunwa zata karu fiye da yadda ake tunani.