Wasu mahara sun kashe mutane 88 a jihar Kebbi, Najeriya a ranar Alhamis, abin da ya ja hankalin gwamnan ya yi alkawarin tura karin jami’an tsaro yayin da rashin tsaro ya ci gaba da yaduwa ba tare da kulawa ba a yankin arewa maso yammacin kasar.
Jerin masu gabatar da shaidu sun kammala bayar da ba’hasi ranar Jumma’a, inda su ka yi ta bayyana yadda aka yi ta tafka almundahana, da kama mutane ba bisa ka’ida ba.
Gwamnatin rikon kwarya a kasar Chadi ta yi watsi da dukkan wani tayin sulhu da ‘yan tawayen kungiyar FACT wadanda suka yi ikirarin halaka shugaba Idriss Deby a farkon makon jiya.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kai wasu hare-hare a wasu cibiyoyi guda uku na kungiyoyin bada agaji na kasa da kasa a arewa maso gabashin Najeriya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gana da hafsoshin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro na Najeriya gabanin ya kama hanyarsa ta zuwa London don gain likita.
Kungiyoyi masu zaman kansu a Najeriya sun dukufa wajen taimakawa gwamnati a kasar don ganin an samar da wata cikakkiyar doka ko tsari da za su sa a dawo da dukiyoyi da aka kwato daga kasashen ketare.
Masana kimiya a Najeriya sun hada alluran rigakafi guda 2 don yaki da annobar cutar korona kamar yadda shugaban kwamitin yaki da cutar kuma sakataren gwamnatin tarrayar Najeriya Boss Mustapha ya sanar.
Kwanaki biyar da kaddamar da rigakafin cutar korona a jihar Kano da ke Najeriya, aikin na fuskantar kalubalen rashin fitowar jama’a.
Wasu 'yan Najeriya biyu sun jingine karatunsu na jami'a don kirkiro manhajar Flux da ake aikawa da karbar kudade daga ko ina a fadin duniya.
Domin Kari