Makomar manufofin shugaban Amurka Joe Biden a sauran shekaru biyu da suka rage a wa’adinsa sun rataya ne kan jam'iyyar da ta samu rinjaye a majalisar dokokin Amurka, yayin da kasar ke dakon sakamakon zaben rabin wa’adin da aka yi ranar Talata.
Dan wasan bayan Sipaniya da kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Gerard Pique ya sanar da yin ritaya daga kwallon kafar kwararru.
Shugabannin hukumar kare hakkin dan adam ta CNDH sun kai ziyara a asibitocin da aka kwantar da mutanen da suka ji rauni a yayin ruwan wutar da jiragen sojan saman Nijar suka yi.
Shugabar kwamitin zabe ta Majalisar Wakilan Najeriya Aisha Jibir Dukku ta jaddada cewa, an tsara zaben 2023 ta hanyar da a ka toshe duk wata kafa ta magudi.
Tsohon Firaimininstan Kasar Pakistan Imran Khan ya samu rauni a wani yunkuri hallakashi a yau Alhamis, yayin da yake jagorantar zanga-zangar kin jinin gwamnati a Islamabad.
Maniyyatan da ba su sami sukunin zuwa aikin hajjin bana ba daga jihar Kano sun fara karbar kudaden su daga hannun hukumar kula da ayyukan hajji ta jihar.
Ten Hang yana kyautata zaton Ronaldo zai kara zura kwallaye idan ya koma yi wa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United wasa.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta ce tana tare kai da fata da Babban Bankin Najeriya CBN, a kan sabbin takardun kudin Naira da za’a fara aiki da su a tsakiyar watan Disamba mai zuwa.
Kasar Kamaru ta sanar da bullar cutar kwalara sakamakon ambaliyar ruwa da ake ci gaba da fuskanta a kan iyakarta da Chadi da Najeriya a arewacin kasar.
Ambaliyar ruwa na ci gaba da addabar al'umomin jihohin yankin Neja Dalta, mussaman ma jihar Bayelsa, inda bayanai suka nuna cewa hanyoyin shiga da abinci sun yanke sakamakon matsalar.
Shugaban kungiyar fafutuka ta Tounrons La Page Internatinale ya jaddada aniyar ci gaba da gwagwarmayar kare muradun kasashen Afirka bayan da ofishin jakadancin Faransa a birnin Yamai ya bada sanarwar soke takardar bizar da ke bashi izinin shiga kasar ta Faransa.
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa dangane da ambaliyar ruwa a Najeriya da ya shafi rayukan maza da mata da kuma yara sama da miliyan 2.8.
Ministan Shari’ar Najeriya ya ce babu maganar sakin shugaban haramtacciyar kungiyar ‘yan awaren Biafara Nnamdi Kanu bayan da wata kotu ta bada umarnin a sake shi.
Kungiayr ASUU ta ce ta janye yajin aikin ne don mutunta umarnin kotun da’ar ma’aikata da na daukaka kara, ba wai don gwamnati ta biya mata dukkanin bukatunta ba tana mai cewa muddin gwamnati bata biya mata bukatunta ba akwai yiyuwar a koma gidan jiya.
Gwamnan jihar Zamfara, Bello Muhammad Matawalle, ya ayyana dokar ta baci a kananan hukumomi uku da wasu garuruwa na jihar, bayan sake barkewar hare-haren ‘yan bindiga.
Jam’iyyar APC mai mulikin Najeriya ta sanar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC cewa Bashir Machina shine dan takararta na Sanatan Yobe ta Arewa, matakin da a karshe ya tabbatar da makomar takarar shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan.
Domin Kari