A lokacin da ake gab da gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a Najeriya, karancin man fetur na ci gaba da ci wa ‘yan kasar tuwo a kwarya, da hakan zai iya zama matsala wajen yin tafiye-tafiye zuwa jihohi don gudanar da zaben.
Wasu 'yan bindiga sun kai wani hari da ake zargin na ramuwar gayya ne a unguwar Wakili da ke karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna, inda su ka kashe mutane da kuma barnata dukiya.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya taya Xi Jinping murnar sake lashe zabe karo na uku don wa’adin shekaru biyar a matsayin shugaban kasa kuma jagoran rundunar sojan China.
A yanzu Mohammed Salah shi ne dan wasan da ya fi ciwa kungiyar Liverpool ta Ingila kwallaye a gasar Premier.
Hukumar Zabe mai zaman kanta a Najeriya ta bayyana Bola Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu.
Jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) ta bi sahun jam’iyyun PDP da na LP wajen kiran da a soke zaben shugaban kasa da na majalisun dokoki da a ka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.
Kwallon farko da Brahim Diaz ya zura a raga tun watan Oktoban bara ta bai wa Milan nasara a kan Tottenham da ci 1-0, a wasan farko na zagayen ‘yan 16 na gasar Zakarun Turai ta Champions League.
Da alama Kylian Mbappe ba zai buga wasan da Paris Saint-Germain za ta yi da Bayern Munich a wasan zagayen farko na ‘yan 16 a gasar cin kofin Zakarun Turai ta Champions League saboda raunin da ya ji a kafarsa.
Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano, ta yanke hukuncin a ranar Alhamis na raba auren shekara 16 tsakanin Asiya Ganduje da Inuwa Uba.
Gwamnatin Kamaru ta fada jiya Talata cewa daga ranar Larabar nan farashin man fetur zai karu da kusan kashi 15 cikin 100, biyo bayan wani sabon matsin lamba da Hukumar Bada Lamuni ta Duniya IMF ta yi game da cire tallafin man fetur.
Gwamnatin jihar Edo da ke kudancin Najeriya ta bada umurnin kama wasu Sarakunan gargajiya biyu tare da wasu mutum biyar da ake zargi da hannu a harin ta’addanci da aka kaiwa jirgin kasa a jihar a ranar 7 ga watan Janairu na 2023.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana kasar Uganda a matsayin wacce ta rabu da cutar Ebola, kwanaki 42 tun bayan samun mutum na karshe da ya kamu da cutar.
Domin Kari